Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-12 11:35:44    
Firaministan kasar Sin ya yi jawabi a majalisar dokokin Japan

cri

Yau da safe, firaministan kasar Sin, Mr.Wen Jiabao, wanda ke yin ziyara a kasar Japan, ya ba da wani jawabin da ke da lakabin "domin sada zumunci da hadin gwiwa" a majalisar dokokin Japan, hakan nan kuma, Mr.Wen Jiabao ya zama kusan kasar Sin na farko da ya ba da jawabi a majalisar dokokin Japan yau da shekaru 22 da suka wuce.


A cikin jawabinsa, Mr.Wen Jiabao ya waiwayi tarihin sada zumunci da ke tsakanin jama'ar Sin da ta Japan a cikin shekaru sama da dubu biyu da suka wuce da kuma wahalhalun da jama'ar kasashen biyu suka sha sakamakon harin da Japan ta kai wa kasar Sin. Ya yi nuni da cewa, a cikin shekaru 35 da aka komar da huldar da ke tsakanin Sin da Japan kamar yadda ya kamata, an sami babban ci gaban huldar da ke tsakaninsu, wanda ya kawo wa jama'ar kasashen biyu moriya ta hakika. Sin da Japan za su amfana daga sada zumunci da juna da ke tsakaninsu, amma dukansu za su yi hasara idan sun yi hamayya da juna. Sada zumunci a tsakanin jama'ar kasashen biyu daga zuriya zuwa zuriya ya dace da bunkasuwar zamani da kuma burin jama'ar kasashen biyu, haka kuma buri ne na kasashen Asiya da na duniya baki daya.


Jiya da yamma, a lokacin da Mr.Wen Jiabao ke yin shawarwari tare da takwaransa na Japan, Shinzo Abe, bangarorin biyu sun kuma tabbatar da ma'anar muhimmiyar huldar abokantaka mai amfana juna, kuma sun amince da kafa tsarin shawarwarin tattalin arziki a tsakanin manyan jami'ansu. Bayan haka, bangarorin biyu sun kuma bayar da hadaddiyar sanarwa.(Lubabatu)