Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya bayar, an ce, jiya Mr. Zhai Jun ya furta ,cewa a kan batun Darfur, bangaren Sudan ya rigaya ya amince da shiri na mataki na uku bisa manufa, wanda Mr. Kofi Annan ya gabatar; Amma ya rike da ra'ayinsa kan wasu takamaiman maganganu.
Mr. Zhai Jun ya ce, a ganin gwamnatin Sudan, ya kamata a bar wani dan Afrika da ya zama kwamandan rundunar sojoji masu kiyaye zaman lafiya; Ban da wannan kuma, ya yi fatan bangarori uku wato Sudan da kungiyar gamayyar Afrika da kuma Majalisar Dinkin Duniya za su yi shawarwari tsakaninsu a game da sikelin rundunar.
Sa'annan Mr. Zhai Jun ya ce, bangaren Sudan har kullum yana fatan al'ummar kasa da kasa za su daukaka ci gaban yunkurin siyasa na daidaita maganar Sudan yayin da suke sauraron ra'ayoyinsa, ta yadda za a aiwatar da shirin Mr. Annan. ( Sani Wang )
|