Mr.Zhai Jun, mai bada taimako ga ministan harkokin waje na kasar Sin, wanda ya kammala ziyarara ba da jimawa ba a kasar Sudan a matsayin manzon musamman na gwamnatin kasar Sin ya yi furuci jiya a nan Beijing, cewa bangaren kasar Sin yana tsayawa kan matsayin bin hanyar shawarwari cikin daidaici don warware batun Darfur na Sudan maimakon kara garkama takunkumi.
A yayin da yake tabo magana kan cewar gwamnatin Amurka na shirin saka wa Sudan takunkumi a game da batun Darfur, ya ce bisa halin da ake ciki yanzu a wannan yanki, bangaren kasar Sin ba ya goyon bayan haka. Sa'annan Mr. Zhai Jun ya kara da, cewa ainihin batun Darfur, magana ce ta bunkasuwa. ' Saboda haka', in ji shi, ' hanya daya tak da za a bi wajen warware wannan batu ita ce farfado da tattalin arzikin wannan yanki'.
Kazalika, ya jaddada, cewa a kan batun Darfur, kasar Sin har kullum tana taka muhimmiyar rawa bisa salon da yake bi. Saboda haka ne, bangaren Sudan ya amince da shirin wanzar da zaman lafiya bisa manufa, wanda tsohon babban sakataren MDD wato Mr. Kofi Annan ya gabatar.
Dadin dadawa, Mr. Zhai Jun ya fadi cewa, wasu mutane na yunkurin kaurace wa taron wasannin Olympic na Beijing domin kai kara ga manufar da gwamnatin kasar Sin take aiwatarwa kan batun Darfur. Lallai rashin hankali ne suka nuna tare da bakin nufi. ( Sani Wang )
|