Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-11 21:29:14    
Sin da Nijeriya

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun Ibrahim Zubairu Othman, dan kungiyar masu sauraren sashen Hausa na rediyon kasar Sin da ke garin Zaria, jihar Kaduna, tarayyar Nijeriya. A cikin wasikar da ya turo mana, ya tambaye mu, wadanne irin gudummowa ne Nijeriya take amfana daga kasar Sin ta hanyar ilmi da masana'antu da lafiya da sufuri da yawon shakatawa da sauransu, shin ko akwai 'yan Nijeriya da ke karatu a kasar Sin? Ko akwai 'yan kasar Sin da ke karatu a Nijeriya? Wane irin amfani Nijeriya take samu dangane da cilla watar dan Adam zuwa sararin sama da kasar Sin take yi? Akwai kayayyakin da aka sana'anta su a kasar Sin da yawa-barbaje ko ina cikin Nigeria, ita kuma kasar Sin wadanne irin abubuwa ne take saye daga Nigeria? Hakika, Sin da Nijeriya aminai ne da ke tallafawa juna da hadin gwiwa da juna har kullum, kuma kasashen biyu sun amfana baki daya daga hadin gwiwar da ke tsakaninsu. Yanzu bari mu dan bayyana muku yadda irin huldar aminci da hadin gwiwa da ke tsakanin Sin da Nijeriya da kuma yadda suke amfana da juna.

Jamhuriyar jama'ar Sin da jamhuriyar tarayyar Nijeriya sun kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu ne a ran 10 ga watan Faburairu na shekarar 1971, tun daga lokacin kuma, huldar da ke tsakanin kasashen biyu sai ta yi ta bunkasa yadda ya kamata. Nijeriya wata muhimmiyar abokiyar ciniki ce ta kasar Sin a Afirka. A shekarar 2005, yawan cinikin da aka yi tsakanin Sin da Nijeriya ya kai dallar Amurka biliyan 2 da miliyan 830, kuma muhimman kayayyakin da Sin ke fitarwa zuwa Nijeriya su ne injuna da kayayyakin lantarki da kuma magunguna, a yayin da Nijeriya ke fitar da danyen mai da gas da sauransu zuwa Sin. Bayan haka, Sin ta kuma sami kwangiloli masu yawa a Nijeriya, ciki har da gine-gine da shimfida hanyoyi da haka rijiyoyi da dai sauransu. A watan Oktoba na shekarar 2006 da ya wuce, kamfanin gine-gine na kasar Sin, wato CCEC ya daddale wata yarjejeniyar shirin gyaran hanyoyin dogo na Nijeriya tare da gwamnatin kasar. Bisa yarjejeniyar, kamfanin zai taimaka wa Nijeriya wajen gina wata hanyar dogo da ke da tsawon kilomita 1315, wadda za ta hada birnin Ikko da kuma birnin Kano. A gun bikin bude aikin, shugaban kasar Nijeriya, Olusegun Obasanjo ya ce, bude aikin da aka yi ya alamanta wani muhimmin ci gaba da Nijeriya ta samu a wajen raya hanyoyin dogo na zamani, kuma zai sa kaimin farfado da tattalin arzikin kasar. Har wa yau kuma, bisa wani labarin da muka samu a kwanan baya, an ce, kamfanin Gezhouba na kasar Sin ya sami kwangilar kafa madatsar ruwan samar da wutar lantarki ta Mombela a Nijeriya, wanda zai kasance aikin samar da wutar lantarki mafi girma da kamfanin Sin ya samu a Afirka.

A fannin ilmi kuma, Sin da Nijeriya suna da yerjejeniyar hadin gwiwar al'adu da kuma yarjejeniyar hadin gwiwar jami'o'i a tsakaninsu. Game da shin ko akwai 'yan Nijeriya da ke karatu a kasar Sin, kuma ko akwai 'yan kasar Sin da ke karatu a Nijeriya, E, gaskiya ne. Tun daga shekarar 1993, bangaren Sin ya fara samar da guraben scholarship ga Nijeriya. A hannu daya kuma, Sinawa su ma suna zuwa jami'o'in Nijeriya domin karatu. Sin da Nijeriya suna kuma gudanar da harkokin musanyar al'adu a tsakaninsu, wadanda suka kara fahimtar juna a tsakanin jama'ar kasashen biyu.

Bayan haka, a bangaren kimiyya kuma, a watan Disamba na shekarar 2004, Sin ta rattaba hannunta kan wata kwangila tare da hukumar binciken sararin samaniya ta Nijeriya. Bisa kwangilar, Sin za ta samar wa Nijeriya wani tauraron dan Adam irin na sadarwa, kuma za ta harba tauraron cikin rokarta mai daukan taurarin dan Adam, kuma za ta gina tashoshi biyu a doron kasa, wato daya a Abuja, babban birnin Nijeriya, dayan kuma a birnin Kash da ke jihar Xinjiang ta kasar Sin, za ta kuma samar da hidima a wajen sarrafa shi da horar da ma'aikata. Wannan tauraron dan Adam zai kasance na farko da jama'ar Nijeriya har ma na shiyyoyin kasashen Afirka da ke kudu da Sahara suke mallaka, wanda zai kyautata harkokin sadarwa da watsa labarai na Nijeriya, har ma na yankunan Afirka da ke kudu da Sahara baki daya, musamman ma a yammacin Afirka.

Bisa bunkasuwar huldar da ke tsakanin Sin da Nijeriya, muna imani da cewa, za a kara samun ci gaba a hadin gwiwar da ke tsakaninsu a fannonin tattalin arziki da ciniki da kimiyya da al'adu da ilmi da dai sauransu duka, kuma tabbas ne za su amfana tare da cin nasara daga irin hadin gwiwar.(Lubabatu)