Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-11 20:45:10    
Kara hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da ciniki buri ne na bai daya na jama'ar Sin da Korea ta Kudu

cri

Ran 11 ga wata da safe, a birnin Seoul, hedkwatar kasar Korea ta Kudu, firayim minista Wen Jiabao na kasar Sin ya yi jawabi kan dangantakar da ke tsakanin Sin da Korea ta Kudu a fannonin tattalin arziki da ciniki, inda ya gabatar da shawarwari 4 kan kyautata hada gwiwa a tsakanin Sin da Korea ta Kudu ta fuskar tattalin arziki da ciniki, ya kuma bayyana cewa, kara hada kai a tsakanin kasashen 2 a fannonin tattalin arziki da ciniki buri ne na bai daya na jama'arsu duka.

Shekarar bana shekara ce ta cikon shekaru 15 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da Korea ta Kudu, kuma ana shirya bikin shekarar yin mu'amala a tsakanin kasashen 2. A cikin shekaru 15 da suka wuce, Sin da Korea ta Kudu sun raya huldar zuminci a tsakaninsu daga dukkan fannoni, sun yi ta kyautata hada kansu ta fuskar tattalin arziki da ciniki, ta haka jama'arsu duka sun ci gajiya sosai. Sin da Korea ta Kudu sun riga sun zama muhimman abokan juna a fannin ciniki. Yanzu ana samun dinkuwar duniya gu daya, shi ya sa ci gaba da kara yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Korea ta Kudu wajen tattalin arziki da ciniki ya zama buri ne na bai daya ga gwamnatocin 2 da jama'ar kasashen 2.

A gaban mutane sama da 300 na Sin da Korea ta Kudu da ayyukansu ke shafar tattalin arziki da ciniki, Mr. Wen ya bayyana cewa, yana fatan Sin da Korea ta Kudu za su yi kokari tare don ci gaban dangantakar tattalin arziki da ciniki a tsakaninsu.

Ya kuma kara da cewa, ya kamata Sin da Korea ta Kudu su kara habaka girman ciniki da sa kaimi ga juna a fannin zuba jari da kyautata hada kansu ta fuskar kimiyya da fasaha da kuma zabura wajen yin nazari kan kasuwar ciniki maras shinge a tsakaninsu cikin hadin gwiwa. Game da kara habaka sikelin ciniki, Ya ce,'Kamata ya yi Sin da Korea ta Kudu su ci gaba da kyautata tsarin ciniki, su kara yin ciniki a fannonin amfanin gona da kayayaykin fasahar zamani da kuma samar da hidima a lokacin da suke ci gaba da tabbatar da samun saurin bunkasuwar cinikin kayayyakin lantarki da na injuna. Gwamnatin Sin ta nuna wa Korea ta Kudu yabo bisa kokarin da take yi wajen rage gibin kudi da Sin ke samu daga wajen ciniki. Kasar Sin tana son kara bude kasuwarta ga Korea ta Kudu da kuma kara sayen kayayyaki daga Korea ta Kudu. Sa'an nan kuma, tana fatan Korea ta Kudu za ta kara sassauta kariyar ciniki domin kafa sharadi mai kyau ga yunkurin shigar kayayyakin kasar Sin a Korea ta Kudu.'

Kazalika kuma, Mr. Wen ya ce, kasar Sin tana fatan masana'antun Korea ta Kudu da suke zuba jari a kasar Sin za su kyautata fannonin da suke zuba kudi a kai. A sa'i daya kuma, kasar Sin tana son yin koyi da fasahohin zamani na Korea ta Kudu da yin mu'ala da ita ta fuskar fasaha da kuma kara hada kai da ita wajen kiyaye muhalli da yin tsimin makamashi.

Mr. Wen ya kuma nanata matsayin kasar Sin na samun ci gaba cikin lumana. A karshe, ya ce,'Ko da yake lokacin ziyarata ya yi kadan, amma na sami sakamako da yawa. Na yi imanin cewa, tabbas ne ziyarata za ta kara sa kaimi kan ci gaban dangantakar zumunci da hadin gwiwa a tsakanin Sin da Korea ta Kudu da daukaka ci gaban tattalin arziki da ciniki a tsakaninsu da kuma kyautata zumunci a tsakanin jama'arsu. Na Gode.'

Jawabin da Mr. Wen ya yi ya sami babban yabo daga masu halartar taron. Malam Sohn Kyung-Shik, shugaban majalisar 'yan kasuwa da masana'antu ta Korea ta Kudu ya bayyana cewa,'Ziyarar da Mr. Wen ya kai wa kasarmu ta nuna cewa, gwamnatin Sin na dora muhimmanci kan raya huldar hadin gwiwa a tsakaninta da kasarmu. Muna sa ran alheri cewa, kasashen 2 za su yi amfani da ziyarar Wen a Korea ta Kudu za su kara raya hadin gwiwa a fannin tattalin arziki. Ina fatan bunkasuwar tattalin arzikin Sin za ta kara ba da gudummowa wajen samun wadata da bunkasuwa tare a Arewa maso gabashin Asiya da kuma duk duniya.'(Tasallah)