Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-11 13:57:17    
Dumama yanayi zai jawo babban bala'i

cri

Barkanku da war haka,a cikin shirinmu na yau na duniya ina labari za mu kawo muku wani bayanin da wakiliyar gidan rediyonmu ta rubuto mana kan batun dumama yanayi. Wakiliyarmu ta ruwaito mana cewa a ran 10 ga wata wata hukuma ta Majalisar Dinkin Duniya da abin ya shafa ta bayar da wani rahoto inda ta ba da cikakken bayani kan illar da dumamar yanayin duniya zai haifa ga rayuwar Bil Adama kai tsaye a nan gaba.Rahoton ya ce idan yanayin duniya na cigaba da dumama,to Bil Adama za su fuskanci sakamakon bala'I mai tsanani a cikin shekaru masu zuwa.

A ran 6 ga wata a birnin Brussels wani kwamitin musamman kan sauyin yanayi tsakanin gwamnati da gwamnati na majalisar dinkin duniya ya bayar da sabon rahoto kan sauyin yanayi na duniya wanda ke da shafuna 1572 da masana kimiyya 441 suka kammala tare.Rahoton da aka bayar ran 10 ga wata takaitaccen rahoto na ran 6 ga wata wanda ya ruwaito wasu ra'ayoyi dangane da illarda dumama yanayin duniya zai haifa ga rayuwar dan Adamu.A cikin rahoton an yi bayani kan makomar nahiyoyin Asiya da Afrika da Oceaniya da kuma bangaren kasashen dake tsibirori na kudancin tekun Pacific wadanda za su fuskantar bala'in dumama yanayin duniya a nan gaba.

Wani sakamako da dumama yanayin duniya zai haifa kai tsaye shi ne raguwar amfanin gona wanda zai barazana rayuwar Bil Adama,kuma tana da illa mafi tsanani ga Asiya wadda ta fi yawan mutane a duniya.Rahoton ya ce idan dumamar yanayin duniya ya karu da awoyi 3 da digo shida,yawan shinkafa da kasar Sin za ta samu zai ragu da kashi biyar cikin kashi dari zuwa kashi sha biyu cikin kashi dari a shekara ta 2050,haka kuma yawan alkamar da Bangaladesh za ta samu zai ragu da kashi daya bisa kashi uku.An kiyasta cewa a shekara ta 2020 mutane kimanin miliyan hamsin za su fuskanci bala'in yunwa,wannan adadi zai karu har zai kai miliyan 132 bayan shekaru talatin.

A shekara ta 2080 mutane miliyan 266za su fuskanci matsalar rashin abinci.lokacin da za a yi fama da yunwa za a kuma samu karancin ruwa.Rahoton ya ce mutane wajen miliyan dari na Indiya za su fuskanci karancin ruwa saboda raguwar ruwan kogin dake kan tsaunukan Himalayan masu kankanra. Kan dumama yanayin duniya,nahiyar Afrika wadda ta fi talauci a duniya ba ta da karfi sosai wajen tinkarar wannan batu za ta fi sha barna.Rahoton ya ce har zuwa karshen karnin nan,mutane wajen biliyan 18 ba su da ruwan sha mai tsabta a nahiyar Afrika,kashi 25 zuwa kashi 40 bisa kashi dari na nau'o'in dabbobi za su bace daga doron kasa,wannan zai jawo lahani mai tsananni ga kasashen Afrika wadanda jigon tattalin arzikinsu shi ne harkar yawon shakatawa.Tare da karin zafin yanayin duniya, cututtuka na kara yaduwa a nahiyar mutanen da za su kamu da cutar zazzabin sauro za su karu da miliyan 80.Ban da wannan kuma kasashen Afrika dake bakin teku za su yi hassarar kashi 14 cikin kashi 100 na jimlar kudin kayayyakin da za a samarwa a gida kai tsaye saboda karuwar ruwayen teku.

Ga kasashen Australiya da New zealand dake a bangaren tekun Oceaniya,idan dumama yanayin duniya za ta tsananta,bala'o'I ire ire za su bulla kamar su fari da ambaliyar ruwa da zaizayar kasa da samun iska mai zafi.Kankara da ke kan tsaunukan Newzealand za ta narke,shi ya sa amfanin gona da za a samu a gabashin da kudancin Australiya da kuma yammancin Newzealand zai ragu sosai,haka kuma cututtuka na yanayin zafi ma za su bullo a can.

Ga kasashen dake kan tsibirorin kudancin tekun Pacific,dumama yanayin duniya za ta lalatamanyan ayyuka na wadannan kasashe,kuma za su kawo barzana ga ruyuwar mutane.Ban da wannan kum abubuwa da dama a cikin teku zasu mutu,kifaye ma za su yi kaura daga can,duk wannan zai jawo barazana ga wadannan kasashe da harkokin shakatawa da kamu kifi a matsayin ginshikan tattalin arzikin kasashensu. Rahoton ya yi nuni da cewa idan aka daina fitar da hayaki mai dumama yanayi a duniya,dumama yanayi ba ta tsaya nan da nan ba.

Wannan halin da muke ciki a yanzu zai cigaba da kasancewa har zuwa shekara ta 2040,a wancan lokaci sakamakon kokarin Bil Adam na yanzu zai iya bayyanu a kai a kai.Rahoton ya yi kira ga kasashen duniya da su tashi tsaye su yi yunkurin rage hayakin dumama yanayi da suke fitarwa da kiyaye muhalli,su bi manufar neman samun dauwamamen cigaba.A sa'I daya kuma rahoton ya bukaci kasashe da lamarin ya shafa da su yi shirye-shiye yadda ya kamata domin tinkarar dumama yanayin duniya.alal misali su tanadi ruwa mai tsabta da kayan abinci da kafa cikakken tsarin kiwon lafiya da tsarin ba da gargadi kafin aukuwar bala'I da rage kafa manyan ayyuka a bakin tekuna. Jama'a masu sauraro,wannan ya kawo karshen shirinmu na yau na duniya ina labari.mun gode muku saboda kuka saurarenmu.