Masu sauraro,ran 1 ga wata,a Melbourne na kasar Australia,aka kammala zama na 12 na gasar cin kofin duniya ta wasan iyo.A gun gasannin da aka yi a cikin kwanaki 16 da suka shige,gaba daya kungiyar `yan wasan kasar Sin ta samu lambobin zinariya 9 da na azurfa 5 da na tagulla 2,yawan lambobin zinariya da ta samu ya zama na hudu a duniya,duk wadannan sun nuna mana cewa `yan wasan kasar Sin suna da babban karfi.A cikin shirinmu na yau,bari mu yi muku bayani kan wannan.
Kamar yadda kuka sani,gasar cin kofin duniya ta wasan iyo ita ce gasar wasan iyo mafi matsayin koli a duniya.Daga ran 14 ga watan jiya,`yan wasa 2200 da suka zo daga kasashe da shiyyoyi 171 sun shiga gasannin da aka shirya a Melbourne,wannan ita ce gasar cin kofin duniya mafi girma da aka shirya a cikin shekaru 34 da suka shige.A gun gasannin da aka yi,kungiyar kasar Amurka ta samun lambobin zinarya 21 da na azurfa 14 da na tagulla 5,ta zama kasa mai samun lambobin yabo mafiya yawa,kungiyar kasar Rasha ta zama lambatu,kuma kungiyar kasar Australia ta zama lambatiri.Kungiyar kasar Sin kuwa ta zama lamba ta hudu.Musamman a gun gasannin tsinduma cikin ruwa da aka shirya,kungiyar kasar Sin ta samun lambobin zinariya 9 daga cikin 10.Wannan shi ne sakamako mafi kyau da ta samu a tarihinta.Kan wannan,jagorar kungiyar wasan tsinduma cikin ruwa ta kasar Sin Zhou Jihong tana ganin cewa,a gun wannan gasar cin kofin duniya ta wasan iyo,`yan wasan kasar Sin sun samun fasahohi da yawa,ta ce, `Lallei,`yan wasan kasar Sin sun samun fasahohi da yawa a gun wannan gasar cin kofin duniya da aka shirya,dalilin da ya sa haka shi ne domin wannan gasa babbar gasa ce,kuma ta yi banban da gasar kofin duniya da ta ba da babbar kyauta.`
A gun wannan gasar cin kofin duniya,`yan wasan tsinduma cikin ruwa daga kasar Sin 14 sun hallarci gasanni,kuma karo na farko ne ga 8 daga cikinsu da su shiga gasar cin kofin duniya,10 daga cikinsu ne ba su taba shiga taron wasannin Olimpic ba.Yawancinsu ba su da fasahar shiga babbar gasa,shi ya sa makasudin kungiyar kasar Sin shi ne don kara samun fasaha,haka kuma za su samun babban sakamako a gun taron wasannin Olimpic da za a yi a birnin Beijing a shekara mai zuwa.Ana iya cewa,sabbin `yan wasan tsinduma cikin ruwa daga kasar Sin sun nuna babban karfi.
Duk da haka,shahararriyar `yar wasa daga kasar Sin kuma zakarar taron wasannin Olimpic Guo Jingjing ta rike zama zakarar gasar tsinduma cikin ruwa daga kan dandamali na mita uku har sau hudu,ta zama `yar wasa wadda ta rike zama zakara sau hudu daya kadai a tarihin gasar cin kofin duniya.Ban da wannan kuma,ta rike zama zakarun gasa tsakanin mata biyu biyu na wasan tsinduma cikin ruwa daga kan dandamali na mita uku tare da `yar wasa daban daga kasar Sin Wu Minxia.Saboda Guo Jingjing ta riga ta tsai da cewa,za ta yi ritaya bayan taron wasannin Olimpic na Beijing,shi ya sa ba za ta sake shiga gasar cin kofin duniya ba,amma ba ta jin bakin ciki kan gasar cin kofin duniya da tarihin wasanta ba.Guo Jingjing ta ce: `Na gamsu da sakamakon da na samu sosai,saboda na riga na shiga gasar cin kofin duniya sau biyar,ba na jin bakin ciki ko kadan ba.`
Amma kungiyar wasan iyo ta kasar Sin ba ta cim ma burinta ba,kodayake ta shiga dukkan gasannin share fage da aka shirya,amma ta shiga zagaye na karshe na gasanni na wasanni goma kawai,gaba daya ta samun lambar azurfa daya kawai.
A halin da ake ciki yanzu,kungiyoyin wasan iyo na kasashe daban daban suna kara kyautatuwa a kwana a tashi,kungiyar kasar Sin kuwa ba ta samun ci gaba ba,wannan ya nuna mana cewa,dole ne sabbin `yan wasan kasar Sin su yi takara da shahararrun `yan wasan kasashen duniya yadda kuma za su samun fasahohi,babban malamin koyar da wasan iyo na kungiyar wasan iyo ta kasar Sin Zhang Yadong ya bayyana cewa, `Ana so a samun sakamako mai kyau,amma idan mun gane karancinmu,sai mu yi iyakacin kokari don warware matsala,a karshe dai mu samun ci gaba,wannan shi ma abu mai daraja ne.Muna fatan za mu samun lambobin zinariya a gun taron wasannin Olimpic da za a yi a birnin Beijing a shekarar 2008 bayan kokarin da muke yi yanzu.`
To,jama`a masu sauraro,karshen shirinmu na yau ke nan,ni Jamila da na gabatar nake cewa,ku zama lafiya,sai makon gobe war haka idan Allah ya kai mu.(Jamila Zhou)
|