Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-10 21:26:08    
An yi bikin bude shagalin "shekara ta 2007 ta yin mu'amala tsakanin Sin da Korea ta Kudu" a birnin Seoul

cri

A ran 10 ga wata da dare, a birnin Seoul, babban birnin kasar Korea ta Kudu, an yi bikin bude shagalin "shekara ta 2007 ta yin mu'amala tsakanin Sin da Korea ta Kudu". Firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao wanda ke yin ziyarar aiki a kasar da kuma takwaransa na kasar Han Duck-Soo sun halarci bikin tare.

A gun bikin, firayim minista Wen ya ba da jawabin cewa, har kullum yin mu'amalar aminci shi ne muhimmin take na dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Korea ta Kudu. Dalilin da ya sa kasashen biyu suka shirya wannan shagali shi ne sabo da suna son sa kaimi ga zumuncin da ke tsakaninsu, da samun bunkasuwa tare ta yin mu'amala tsakaninsu, ta yadda za a iya samar da wata makoma mai kyau ga bunkasuwar kasashen biyu a nan gaba.(Kande Gao)