Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-10 21:21:24    
Wen Jiabao ya yi shawarwari da shugabannin Korea ta Kudu bi da bi

cri

Ran 10 ga wata, a birnin Seoul, hedkwatar kasar Korea ta Kudu, firayim minista Wen Jiabao na kasar Sin ya yi shawarwari da shugaba Roh Moo-hyun na kasar da firayim minista Han Duck-Soo na kasar bi da bi. Shugabannin kasashen 2 dukkansu sun bayyana cewa, suna son yin amfani da damar cikon shekaru 15 da kulla huldar jakadanci a tsakanin kasashen 2 da kuma bikin shekarar yin mu'amala a tsakanin kasashen 2, don kara tuntubar juna bisa manyan tsare-tsare da sa kaimi kan hadin gwiwar moriyar juna a tsakaninsu, ta haka bangarorin 2 za su yi ta samun sabon ci gaba a fannin raya dangantakarsu.

A gun shawarwarin da ya yi tare da shugaba Roh Moo-hyun, Mr. Wen ya ba da shawarar cewa, ya kamata bangarorin 2 za su yi ta yin cudanya a tsakanin manyan jami'ai da kyautata hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki da sa kaimi kan yin mu'amalar abubuwan da ke shafar dan Adam da kara yin tattaunawa da taimakon juna a kan al'amuran duniya da shiyyar da suke ciki. A nasa bangaren kuma, Mr. Roh ya amince da ra'ayi da shawarar da Mr. Wen ya bayar kan raya huldar da ke tsakanin kasashen nan 2, ya kuma yi imani cewa, ziyarar da Mr. Wen yake yi za ta raya huldar Sin da Korea ta Kudu zuwa wani sabon mataki.

A lokacin da yake yin shawarwari da takwaransa na Korea ta Kudu Han Duck-Soo, Mr. Wen ya ce, kamata ya yi bangarorin 2 su mai da hankulansu kan shirya bukukuwan murnar cikon shekaru 15 da kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu da shekarar yin mu'amala a tsakaninsu don sa kaimi kan yin mu'amala da hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da ciniki da al'adu da aikin ba da ilmi da harkokin yawon shakatawa da dai sauransu, sa'an nan kuma ya kamata su kara taimakon juna a kan batun nukiliya na zirin Korea da zabura bangarori daban daban da su dauki matakai tun da wuri, ta haka za su ba da gudummowa wajen tabbatar da rashin nukiliya a zirin Korea da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan shiyya cikin sauri.

A nasa wajen kuma, Mr. Han ya ce, Korea ta Kudu za ta yi kokari tare da kasar Sin wajen shirya bikin shekarar yin mu'amala a tsakaninsu yadda ya kamata. Ta kuma yi fatan sa kaimi kan hadin kai da kasar Sin ta fuskar ciniki da aikin sadarwa da makamashin nukiliya da hanyoyin dogo, kazalika kuma za ta gama kanta da kasar Sin wajen kara tuntuba da taimakon juna a kan al'amuran duniya da shiyyar da suke ciki.(Tasallah)