Shekarar da muke ciki shekara ce ta cikon shekaru 35 da kafuwar dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Japan. Sabo da haka, shugabannin kasashen biyu sun tabbatar da cewa, shekarar da muke ciki "shekara ce ta musayar al'adu da wasannin motsa jiki a tsakanin Sin da Japan." Tun da yake ne, kasashen biyu suna shirya bukukuwan al'adu da na wasannin motsa jiki iri iri domin kara yin musanye-musanye da fahimtar juna a tsakanin jama'arsu
Mr. Zhang Aiping, mataimakin direktan hukumar yin cudanya da kasashen waje ta ma'aikatar al'adu ta kasar Sin ya bayyana dalilin da ya sa aka shirya wannan "Shekarar yin musayar al'adu da wasannin motsa jiki a tsakanin Sin da Japan". Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai kan wannan biki. "A shekarar da ta gabata, lokacin da yake kawo wa kasar Sin ziyara da ya hawansa kan mukamin firayin ministan kasar Japan, Mr. Shinzo Abe da takwaransa na kasar Sin Wen Jiabao sun sami ra'ayi daya game da wannan shekarar yin musayar al'adu da wasannin motsa jiki a tsakanin Sin da Japan domin taya murnar cikon shekaru 35 da kafuwar dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu. Gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai kan wannan al'amari. Ta kafa wani kwamitin da ke hade da ma'aikatan gwamnati 7 da ke karkashin jagorancin minista Sun Jiazheng na al'adu na kasar Sin domin shirya wannan shagali. Ana cike da imani cewa, za a sanya shekarar da muke ciki da ta zama shekarar da jama'ar kasashen biyu za su iya kara fahimtar juna da sada zumunta da yin musanye-musanye a tsakaninsu."
A waje daya kuma, bangaren kasar Japan na mai da hankali sosai kan wannan shekara. A watan Disamba na shekarar da ta gabata, kasar Japan ta kuma kafa wani kwamitin shirya "Shekarar yin musayar al'adu da wasannin motsa jiki a tsakanin Japan da Sin" domin aiwatar da dukkan harkokin da ke shafar wannan shagali. Mr. Kono Akira, mataimakin direktan hukumar kula da harkokin da ke shafar wannan shagali na kwamitin bangaren Japan ya bayyana wa wakiliyarmu tunanin yadda bangaren Japan zai shirya wannan shagali. Mr. Kono Akira ya ce, "Muna fatan za mu iya bayyana wa jama'ar Sin wata sabuwar Japan da jama'arta. A waje daya, muna fatan mutanen Japan masu dimbin yawa za su samu damar fahimar al'adun kasar Sin, ta yadda za iya kara yin musanye-musanye da fahimtar juna a tsakanin kasashen biyu, musamman a tsakanin matasa na kasashen biyu."
Tun daga watan Disamba na shekarar bara zuwa watan Janairu na shekerar da muke ciki, kwamitin zartaswa na Japan ya fara neman alama da taken wannan shagali a kan tasoshin shafuffukan internet na gwamnatin Japan. A ran 12 ga watan Maris, an sanar da cewa, alamar zuciya da madam Kagaya Miyuki ta kasar Japan ta zana da kuma ke hade da farkon harrufan China da Japan. Harrufa C tana hagu, harrufa J tana dama, an hada su tare sai suka zama wata alamar zuciya. Madam Kagaya Miyuki ta ce, "Da farko dai, dole ne a bayyana zumuncin da ke kasancewa a tsakanin Sin da Japan. Sannan kuma dole ne wannan alama tana nasaba da kasashen biyu, amma ba alama ce da take yaduwa a cikin wani lokaci kawai ba."
Taken wannan shagalin da aka zaba shi ne "Muna jiran sabuwar makoma a cikin zuciyarmu" da Mr. Huang Xinguo na kasar Sin ya rubuta. Lokacin da yake bayyana yadda ya samu wannan take, Mr. Huang ya ce, "Lokacin da nake nazarin muhimmin taken wannan shagali, ina ganin cewa, shekarar da muke ciki shekara ce ta cikon shekaru 35 da kafuwar dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Japan, ya kamata bangarorin biyu su yi koyi da tarihi domin neman wata sabuwar makoma, kuma za a iya kara yin musanye-musanye a tsakaninsu daga zuciya."
Bisa shirin da aka tsara, a cikin wannan shekarar yin musayar al'adu da wasannin motsa jiki a tsakanin Sin da Japan, za a shirya bukukuwa fiye da dari 1, muasmman za a kara shirya bukukuwan kara yin musanye-musanye a tsakanin matasa da kafofin watsa labaru da fasahohin zane-zane iri iri a tsakanin kasashen biyu. (Sanusi Chen)
|