Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-10 20:52:30    
Wurin shakatawa na tsaunukan Alishan da tabkunann Riyuetan na Taiwan

cri

Salamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin, wanda mu kan gabatar muku a ko wace ranar Talata. Kamar yadda muka saba yi, da farko dai, za mu karanta muku wasu abubuwan da ke wurin shakatawa na tsaunukan Alishan da tabkunan Riyuetan da ke lardin Taiwan na kasar Sin, daga bisani kuma, sai wani bayanin musamman, inda za mu gabatar muku da wani titin al'adu da ke nan Beijing, wanda ke da sigogin musamman na tarihi, sunansa Liulichang'.

A arewa maso gabashin gundumar Jiayi ta lardin Taiwan na kasar Sin, ya kasance da tsaunukan Alishan, wadanda suka hada da manyan duwatsu 18, kamar su babban dutse na Dawuluanshan da na Jianshan da na Zhushan da na Tashan da dai sauransu. Tsayin tsaunukan Alishan ya kai misalin mita 1,000 zuwa mita 2,500 daga kan leburin teku. Babbar kololuwarsu ita ce babban dutse na Datashan mai tsayin misalin mita 2,663 daga kan leburin teku. Tsaunukan Alishan sun yi suna ne saboda ni'imtattun wurare, wurin nan wurin shakatawa ne mafi kyau, musamman ma a lokacin zafi. Yawan zafi ya sha bamban a tsakanin gindin tsaunukan da kololuwarsu. Ana sanyi a gindin tsaunukan, amma a kololuwar, ana zafi sosai. An mayar da tsaunukan Alishan a matsayin gidan albarkatun gandun daji. Wurare masu ni'ima da kyan gani suna rufe wadannan tsaunuka masu tsayi. Masu yawon shakatawa suna iya ganin abubuwan mamaki 5 a nan, wato hanyar dogo mai tsawon misalin kilomita 72 da aka shimfida bisa tsaunukan da gandun daji da tekun gajimare da fitowar rana da kuma hasken rana a lokacin da yake faduwa. Sun kuma iya more idanunsu da sauran kyawawan wurare.

Tabkunan Riyuetan sun shahara ne a matsayin wata alama daban ta Taiwan. Karamin tsibiri na Guanghua ya zama iyaka a tsakanin tabkuna 2, takbi na arewa ya yi kama da rana, wato Taiyang ko kuma Ri a Sinance, na kudu kuma ya kasance kamar wata, wato Yueliang ko kuma Yue a bakin Sinawa. Shi ya sa ake kira wadannan tabkuna 2 da Riyue ne saboda sifofinsu masu ban mamaki. Wadannan tabkuna 2 tabkuna ne mafi girma a lardin Taiwan. Mutane su kan kwatanta wadannan kyawawan tabkuna 2 da wani shahararren tabki daban na kasar Sin, wato tabkin Xihu na birnin Hangzhou na lardin Zhejiang. Masu yawon shakatawa suna ta kai ziyara a nan a ko wace shekara saboda ni'imtattun wurare masu kyan gani. Ban da wadannan tabkuna 2, wadanda aka sifanta kyan ganinsu kamar yadda zane-zane suke, akwai sauran wuraren shakatawa da yawa da ke jawo hankulan masu yawon shakatawa, al al misali, gidan ibada na Wenwu da na Xuanzang da karamin tsibiri na Guanghuadao da sauran makamantasu.