Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-10 14:27:58    
Firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya isa kasar Korea ta kudu

cri

Bisa gayyatar da shugaba Roh Moo-hyun na kasar Korea ta kudu ya yi masa, ranar 10 ga wata, firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya isa birnin Soul, babban birnin kasar, don fara yin ziyarar aiki a kasar.

Shekarar da muke ciki shekara ce ta cika shekaru 15 da kasashen Sin da Korea ta kudu suka kulla huldar diplomasiya, da kuma "shekarar yin mu'ammala a tsakanin Sin da Korea ta kudu". A cikin jawabin da ya yi a rubuce a filin jiragen sama, Mr. Wen Jiabao ya bayyana cewa, tun bayan da kasashen biyu suka kulla huldar diplomasiya, bangarorin biyu sun samu bunkasuwa da sauri wajen yin mu'ammala da hadin kai a fannoni daban daban, sun kawo babbar moriya ga jama'ar kasashen biyu, kuma sun ba da taimako sosai kan zaman lafiya da bunkasuwa a shiyyar. Kara sai kaimi da bunkasa dangantakar abokantaka ta hadin kai da ke tsakanin kasashen Sin da Korea ta kudu a dukan fannoni, manufa ce da gwamnatin kasar Sin ke tsayawa. Dalilin da ya sa ya kai ziyara a Korea ta kudu shi ne, kara yin musayan ra'ayoyi tare da Korea ta kudu, da sa kami ga hadin kai na samun moriyar juna, da kuma habaka moriya iri daya a tsakaninsu. Ya bayyana cewa, yana sa ido ganin a karkashin kokarin da bangarorin biyu suke yi, ziyarar za ta kara sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar abokantaka ta hadin kai da ke tsakanin Sin da Korea ta kudu a dukan fannoni. (Bilkisu)