Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-09 22:14:18    
Wata kungiyar yin mu'amala tsakanin matasa da ke kula da ayyukan ba da ilmin jami'i ta kasar Sin

cri

An kafa kungiyar yin mu'amala tsakanin matasa ta kasar Sin ne a shekara ta 2004 a karkashin goyon bayan kungiyar kula da haihuwa bisa shiri ta kasar Sin da kuma asusun kula da yawan mutane na MDD, kuma membobinta su matasa ne daga wurare daban daban na kasar Sin. Li Haimin wanda ya zo daga birnin Yangquan na lardin Shanxi da ke arewacin kasar Sin yana daya daga cikin membobin farko na kungiyar. Ya gaya wa wakilinmu cewa, nufin kafa kungiyar yin mu'amala tsakanin matasa ta kasar Sin tana da takamaiman dalili, wato dukufa kan yada ilmin jima'i a wurare daban daban na kasar Sin musamman ma a wurare inda tattalin arzikinsu yana baya baya domin taimaka wa matasan wuraren nan wajen warware matsalolin da ke fuskanta a zaman rayuwarsu. Amma bayan da aka tafiyar da ayyukan kungiyar, ma'aikatan kungiyar sun gano cewa, yana da matukar wuya wajen tafiyar da su. Kuma Mr. Li ya bayyana cewa, lokacin da ya fara yin furofaganda kan ilmin jima'i a garinsa, an kawo masa cikas sosai. Ya kara da cewa,

"A kan ji nauyin bayyana maganar jima'i a fili a garinmu. Mun taba yin gwajin tafiyar da ayyukanmu na ba da ilmin jima'i ga matasan da ke aiki a wata masana'anta, amma mun ci tura. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da shugabansu ya nuna rashin amincewa sosai wajen yin magana tare da matasa kan jima'i. Daga baya kuma mun lallashe shi har sau da yawa, a karshe dai ya amince da tura wakilai biyu na matasa da su shiga kwas din horaswa da muka shirya."

Ban da wannan kuma Mr. Li ya bayyana cewa, irin wannan al'amari ya kan faru. Amma a karkashin kokarin da ma'aikatan kungiyar yin mu'amala tsakanin matasa ta kasar Sin ke yi, kungiyar ta yi suna a gwargwado ta hanyoyin rarraba takardun furofaganda da shirya kwas din horaswa a cikin shekaru biyu da suka gabata, yanzu matasa masu yawa sun samu ilmin kiwon lafiya na lokacin balaga ta shiga harkokin da suka shirya, ta yadda suna iya warware wasu matsalolin da suke fuskanta a fannin hayayyafa.

Wu Liping da ta zo daga gundumar Deqing ta lardin Zhejiang da ke gabashin kasar Sin tana daya daga cikin membobin kungiyar. Ita wata daliba ce ta wata makarantar sakandare ta gundumar Deqing. Ta kafa kungiyar bayar da ilmin jima'i daga abokan karatu domin yada ilmin jima'i da ya dace ta yin mu'amala tsakaninsu.

Lokacin da Wu Liping ta kaddamar da ayyukan kungiyar, ta gamu da wahaloli masu yawa. Kuma ta gaya mana cewa, lokacin da ta shirya harka a cikin makaranta a karo na farko, mutane uku ko hudu ne kawai suka shiga a ciki. Ko da haka ba ta yi watsi da wannan aiki ba. A cikin wadannan shekaru biyu da suka gabata, sabo da kokarinta, matasa fiye da goma sun shiga kungiyar samun ilmin jima'i daga abokan karatu. A waje daya kuma kungiyar ta shirya harkokin ba da ilmin jima'i a sauran makarantum wurin domin matasa mafi yawa su sa hannu a cikin wannan aiki. Pang Can ita ce wata abokiyar karatu ta Wu Liping, har kullum tana shiga harkokin da kungiyar samun ilmin jima'i daga abokan karatu ta shirya, kuma tana ganin cewa, ta samu karuwa sosai. "Bayan da na shiga harkokin da abin ya shafa, na fahimtar cewa, lokacin balaga lokaci ne mafi muhimmanci na duk rayuwar dan Adam, musamman ma a fannonin jima'i da hayayyafa."

Ta shirya kwas din horaswa da ayyukan ba da ilmin jima'i daga abokan karatu da sauran harkoki, kungiyar yin mu'amala tsakanin matasa ta kasar Sin tana ta samun kyautatuwa. Ya zuwa yanzu ta riga ta kafa hukumomin da abin ya shafa a gundumomi 30 na duk fadin kasar Sin. Sabo da haka matasa masu yawa sun samu damar samun ilmin jima'i da hayayyafa.

Bugu da kari kuma kungiyar yin mu'amala tsakanin matasa ta kasar Sin ta hada kai tare da hukumomin gwamnatin kasar Sin da kungiyoyin zamantakewar al'ummar Sin da abin ya shafa domin samun amincewa da goyon baya daga zamantakewar al'umma. A cikin sabbin sayyukan taimaka wa kasar Sin da asusun yawan mutane na MDD ya bayar ba da jimawa ba, an nuna goyon baya ga kungiyar yin mu'amala tsakanin matasa ta kasar Sin wajen ci gaba da samun bunkasuwa. Kuma Madam Mariam Khan, mataimakiyar wakilin ofishin asusun da ke kasar Sin ta bayyana cewa, "Matasa suna da basira, suna da karfi wajen ba da taimako ga kansu, musamman ma a fannonin jima'i da hayayyafa."

Kungiyar fararen hula mafi girma wajen kula da yin haihuwa bisa shiri da kuma ba da ilmin jima'i ta kasar Sin wato kungiyar yin haihuwa bisa shiri ta kasar Sin tana ba da jagoranci da nuna goyon baya ga ayyukan kungiyar yin mu'amala tsakanin matasa ta kasar Sin har kullum. Kuma Madam Li Yanqiu, babbar sakatariyar kungiyar ta bayyana cewa, "ina ganin cewa, muddin matasa sun shiga ayyukan da kungiyarmu ta tafiyar, sai za mu iya biyan bukatunsu yadda ya kamata." Kande Gao)