Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-09 22:08:29    
Takaitaccen bayani game da kabilar Tu

cri

'Yan kabilar suna zama a yankunan da ke gabashin lardin Qinghai, amma ke kudu da kogin Huangshui da yankunan da ke bakin kogin Rawaya. Galibinsu suna zama a gundumar Huzhu ta kabilar Tu mai gashin kanta da gundumomin Minhe da Datong da Tongren na lardin Qinghai, wasu kuma suna zama a gundumar Tianzhu ta kabilar Tibet mai cin gashin kanta ta lardin Gansu. Bisa kididdigar da aka yi a duk fadin kasar Sin a shekara ta 2000, yawan mutanen kabilar Tu ya kai kimanin dubu 240. Suna amfani da yaren Tu. A da, suna amfani da kalmomi da harufan harshen Sinanci, amma a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, an kago wasu harufan yaren Tu, ana kuma gwajin amfani da su.

Kabilar Tu tana da hulda sosai da kabilar Mongoliya. Wasu mutanen kabilar Tu sun kuma fadi cewa, kakanin-kakaninsu 'yan kabilar Mongoliya ne.

A da, 'yan kabilar Tu suna aiwatar da sana'ar kiwo, amma daga baya, sannu a hankali ne sun fara yin aikin gona da sana'ar kiwo tare.

Bayan da 'yan kabilar Tu suka sami 'yancin kai a watan Satumba na shekarar 1949, an yi gyare-gyare sosai kan tattalin arziki da zaman al'ummar kabilar. A shekarar 1954, gwamnatin kasar Sin ta kafa gundumar Huzhu ta kabilar Tu mai cin gashin kanta da wasu kananan hukumomin kabilar Tu. Tun daga wancan lokaci ne, tattalin arziki da zaman al'ummar yankunan kabilar Tu sun yi ta samun cigaba cikin sauri. Ya zuwa yanzu, an riga an shimfida hanyoyin mota da samar da wutar lantarki a yawancin kauyukan 'yan kabilar Tu. Zaman rayuwar jama'ar kasar Sin ta samu kyautatuwa sosai. Harkokin al'adu da ilmi da kiwon lafiya ma sun samu cigaba kwarai. Yanzu, an riga an kafa masana'antun firamare da na sakandare har da kwalejin horar da malamai tare da wasu asibitoci da dakunan jiyya a gundumar Huzhu ta kabilar Tu mai cin gashin kanta.

Jama'ar kabilar Tu sun kware sosai kan waka da raye-raye. Al'adun jama'a suna da ban sha'awa kwarai. Ana yada adabin jama'a ta hanyar baki. Suna kuma da wakoki iri iri ciki har da wakokin gida da na aiki.

Abincin da 'yan kabilar Tu suke ci yana nasaba da sana'ar aikin gona da ta kiwo sosai. Suna dacewa da cin abincin da aka yi da garin alkama da nama, amma ba su cin ganye da yawa, kuma suna shan ti da aka yi da madara.

'Yan kabilar Tu suna gina gidajensu a wuraren da ke dab da duwatsu ko a bakin kogi. Suna da ladabi sosai, musamman suna girmama dattawa. Idan wani bako ya isa wani gidan dan kabilar Tu, sai mai gida ya ce, "Bako ya zo, sai alheri ya iso."

'Yan kabilar Tu suna bin addinai iri iri, ciki har da addinin Dao na kasar Sin da addinin Buddha. (Sanusi Chen)