Ran 8 ga wata, kafofin watsa labaru na kasar Cote D'Ivoire sun ruwaito wani labarin kungiyar aiki ta majalisar dinkin duniya da ke a kasar na cewa, sojojin kiyaye zaman lafiya na majalisar dinkin duniya da sojojin kasar Faransa za su fara janye jikinsu daga kasar tun ran 16 ga wata sannu a hankali. A ran 7 ga wata kuma, an kammala aikin kafa sabuwar gwamnatin wucin gadi ta kasar Cote D'Ivoire da ke karkashin shugabancin Guillaume Soro, sabon firayim ministan kasar. Manazarta suna ganin cewa, duk wadannan sun nuna cewa, gwamnatin kasar da dakaru masu adawa da gwamnatin suna aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da aka daddale a tsakaninsu a farkon watan jiya a tsanake, sa'an nan kura tana lafawa a kasar sannu a hankali.
Bisa sulhuntawar da kungiyar tarayyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika wato ECOWAS ta yi, tun daga watan Febrairu da ya wuce, Laurent Gbagbo, shugaban kasar Cote D'Ivoire da Guillaume Soro, shugaban siyasa na dakaru masu adawa da gwamnatin sun shafe wata daya suna tattaunawa a tsakaninsu kai tsaye. A ran 4 ga watan jiya, a karkashin shugabancin Blaise Compaore, shugaban kasar Burkina Faso kuma shugaban kungiyar ECOWAS, shugaba Gbagbo da Soro sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya a birnin Ouagadougou, hedkwatar kasar Burkina Faso. Bisa yarjejeniyar, bangarorin biyu sun amince da kafa sabuwar gwamnati a cikin wani gajeren lokaci mai zuwa, da soke yanki da aka kebe don girke sojojin kasashen waje, da maido da bincike matsayin mazauna da kwance damara, da yi watsi da kungiyoyin dakaru farar hula da kuma kafa dayatacciyar rundunar sojoji ta yadda za a yi shirin babban zabe tun da wuri.
Manazarta suna ganin cewa, bangarori biyu masu gaba da juna na kasar Cote D'Ivoire sun daddale wannan yarjejeniya ne ta hanyar yin tattaunawa a tsakaninsu kai tsaya kuma bisa burinsu, sa'an nan a karo ne na farko suka gabatar da hakikanin jadawarin ayyuka daban daban da za a yi don samar da zaman lafiya. Sabo da haka yarjejeniyar ta sami babban yabo daga bangarori daban daban da al'amarin ya shafa.
Abin da ya fi faranta rayukan mutane shi ne, gwamnatin kasar da bangaren adawa dukanninsu suna aiwatar da abubuwa da aka tanada a cikin yarjejeniyar a kai a kai. A farko, an fara gudanar da harkokin kafa sabuwar gwamnati cikin sauri. A ran 29 ga watan jiya, shugaba Gbagbo ya nada Soro, shugaban siyasa na dakaru masu adawa da gwamnati da ya zama firayim ministan kasar, kuma a ran 4 ga wata, Soro ya hau kujerarsa a hukunce. A ran 7 ga wata, an sanar da kafa sabuwar gwamnatin wucin gadi ta karar, shugaba Gbagbo ya nada sabbin ministoci da yawansu ya kai 32. Ban da wadannan kuma, an sami ci gba wajen soke yanki da aka kebe don girke sojojin kasashen waje. A kwanan baya, kungiyar aiki ta majalisar dinkin duniya da ke a kasar Cote D'Ivoire ta bayar da labarin cewa, sojojin kiyaye zaman lafiya na majalisar dinkin duniya 7,800 da sojojin Faransa 3,500 wadanda ke girke a kasar za su fara janye jikinsu daga kasar tun daga ran 16 ga wata, sa'an nan za a soke yankin musamman da aka kebe don girke wadannan sojoji a tsakanin arewa da kudu. Bisa irin wannan ci gaba da aka samu, an fara sa ran alheri ga zaman lafiya da za a tabbatar a kasar.
Amma wajibi ne, a yi na'am da cewa, ya zuwa yanzu dai, yana kasancewa da matsaloli masu yawa yayin da ake daidaita batun kasar cikin lumana. Na farko, ba a bayyana abubuwa filla-filla a kan ikokin firayim minista Soro ba. Na biyu, za a gamu da matsaloli masu sarkakiya yayin da ake bincike matsayin mazauna, da kwance damara, da kafa dayantacciyar rundunar sojoji, yanzu kuma ba a fara yin wadannan harkoki ba tukuna. Na uku, hargitsi da yaki da aka shafe shekaru da yawa ana yinsu sun haifar da matsalolin zaman jama'a da yawa a kasar, kamar sabane-sabane masu tsanani da ke kasancewa a tsakanin kabilu daban daban, halin da ake ciki dangane da zaman lafiyar jama'a yana tabarbarewa, kuma aikin samar da kayayyaki yana baya-baya, kai lalle ne za a sha wahalhalu wajen daidaita wadannan matsaloli. (Halilu)
|