Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-06 18:57:38    
Firaministan Sin yana fatan ziyararsa za ta sa kaimi ga hadin gwiwar aminci da ke tsakanin Sin da Koriya ta kudu

cri

Tun daga ranar 10 ga watan nan da muke ciki, firaministan kasar Sin, Mr.Wen Jiabao zai fara ziyarar aiki a kasar Koriya ta kudu. A yayin da yake hira da manema labaru na kasar Koriya ta kudu kafin ziyarar, Mr.Wen Jiabao ya ce, yana fatan wannan ziyararsa za ta karfafa dankon zumuncin da ke tsakanin jama'ar Sin da ta koriya ta kudu da kuma kara sa kaimi ga hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu."na dade ina son yin wannan ziyarar, kuma zan kai ziyarar ne tare da sada zumunci da hadin gwiwa, ina son ku iya isar da gaishe-gaishe da fatan alheri da jama'ar kasar Sin ke nuna wa jama'ar Koriya ta kudu."

A lokacin da yake hira da manema labaru a ranar 5 ga wata, da farko, manema labaru na kasar Koriya ta kudu sun yi wa firaministan kasar Sin wasu tambayoyi dangane da halin da zirin Koriya ke ciki. Mr.Wen Jiabao, firaministan kasar Sin ya ce, Sin tana fatan bangarori daban daban za su kara yin shawarwari a gun shawarwarin da ke tsakanin bangarori shida wanda ke da burin sa kaimin daidaita batun nukiliyar zirin Koriya, ta yadda za a samar da sharuda masu kyau ga kafa tsarin zaman lafiya a zirin Koriya. Ya kuma jaddada cewa, kamata ya yi Koriya ta kudu da ta arewa su da kansu su daidaita batun zirin Koriya cikin lumana.Ya ce,"muna fatan koriya ta kudu da ta arewa za su bi hanyar yin shawarwari, kuma su kara tuntubar juna da kara amincewa da juna da kuma karfafa huldar da ke tsakaninsu, kuma bisa wannan tushe, su tabbatar da dinkuwar kasa bisa karfin kansu da kuma cikin lumana."

Mr.Wen Jiabao ya kai wannan ziyara ne a daidai lokacin cika shekaru 15 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da Koriya ta kudu. Ko da yake wannan ba dogon lokaci ba, amma duk da haka, bunkasuwar huldar da ke tsakanin kasashen biyu tana kasancewa cikin wani kyakkyawan hali har kullum, musamman ma hadin gwiwar ciniki da ke tsakaninsu ya fi daukar hankulan jama'a. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yawan cinikin da ke tsakanin kasashen biyu ya zarce dallar Amurka biliyan 130 a shekarar 2006. A yayin da yake hira da manema labaru, Mr.Wen Jiabao ya ce, bunkasuwar tattalin arzikin duniya bai daya ya shigar da huldar ciniyya da ke tsakanin Sin da Koriya ta kudu cikin wani sabon mataki na habaka fannoni da kyautata inganci da kuma fuskantar kalubale tare. Ya ce,"A ganina, abin da ya fi muhimmanci a wajen habaka fannoni shi ne inganta hadin gwiwa a fannonin makamashi da kiyaye muhalli da kudi da labarai. Sa'an nan, kyautata inganci shi ne sa kaimi ga bunkasuwar cinikin da ke tsakanin bangarorin biyu cikin dorewa da kuma daidaici, kuma Sin da Koriya ta kudu ko wacensu su ba da fifikonsu, su kyautata ingancin hadin gwiwar tattalin arziki. Bayan haka, fuskantar kalubale tare na nufin ya kamata bangarorin biyu su kara shawarwari da hadin gwiwa a cikin kungiyar APEC da kuma tsakanin kasashen kungiyar ASEAN da kasashen Sin da Japan da Koriya ta kudu da taron kolin gabashin Asiya da sauransu."

Sin da Koriya ta kudu suna da dadadden tarihi na yin mu'amalar al'adu. A cikin 'yan shekarun baya, Sin ta shigo da fina-finai da dama dangane da ala'dun Koriya ta kudu, wadanda suka sami karbuwa sosai daga wajen jama'ar Sin, musamman ma matasa. A hannu daya kuma, koyon Sinanci da kara fahimtar al'adun Sin yana zamowa ruwan dare a Koriya ta kudu. Don kara sa kaimi ga musanyar al'adu da ke tsakanin Sin da Koriya ta kudu, kasashen biyu sun kuma tsai da shekarar da muke ciki a matsayin "shekara ta yin mu'amala a tsakanin Sin da Koriya ta kudu."(Lubabatu)