Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-06 18:54:22    
Gwamnatin birnin Beijing na kokarin tabbatar da ingancin kiwon lafiyar jama'a a lokacin da ake gudanar da taron wasannin Olympic

cri

Jama'a masu saurare, mun san cewa, a kowane lokacin da ake gudanar da gagaruman gasanni kamar taron wasannin Olympic, ban da gasanni masu ban al'ajabi, wassu abubuwan dake waje da gasannin su ma sukan janyo hankulan mutane. Aikin tabbatar da ingancin kiwon lafiyar jama'a, wani muhimmin abu ne dake cikinsu domin ba ma kawai yana jibintar lafiyar jikin 'yan wasa da masu koyar da 'yan wasa, har ma yana da nasaba sosai da jama'ar wuri,inda ake gudanar da gasanni. Da yake ranar gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008 na kusantowa, shi ya sa mutane suka fi mayar da hankali kan aikin tabbatar da ingancin kiwon lafiyar jama'a a lokacin da ake gudanar da wannan gagarumin taro.

A gun wani taron ganawa da manema labaru da aka shirya kwanan baya ba da jimawa ba, shugaban hukumar kula da harkokin kiwon lafiya ta birnin Beijing wato Mr. Jin Dapeng ya fayyace, cewa bisa fasahohin da aka samu a da, gwamnatin birnin Beijing ta rigaya ta aza harsashi mai inganci na tabbatar da ingancin kiwon lafiyar jama'a domin taron wasannin Olympic sakamakon ayyukan share fage da kuma gwaje-gwajen da aka yi. Mr. Jin ya furta, cewa ' makasudin karshe na aikinmu, shi ne gudanar da wani gagarumin taron wasannin Olympic da kuma barin wani kayan gado na koshin lafiya na taron wasannin Olympic, wato ke nan ' Beijing na da koshin lafiya kuma birni na da koshin lafiya'.

Sa'annan Mr. Jin Dapeng ya bayyana, cewa wani aiki mafi muhimmanci dake cikin ayyukan tabbatar da ingancin kiwon lafiyar jama'a domin taron wasannin Olympic, shi ne rigakafi da shawo kan munanan cututtuka masu yaduwa. Sanin kowa ne, yanzu wassu cututtuka kamar cutar murar tsuntsaye wadanda mutane da dabbobi sukan kamu da su tare, sun rigaya sun zama munanan cututtuka dake yin illa ga dukkan 'yan adam. Ban da wannan kuma, cutar SARS da ciwon SIDA su ma sun kasance matsaloli masu tsanani ne dake gaban duk duniya. Birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin ce. Akwai mutane masu dimbin yawa da za su zo nan Beijing a duk tsawon lokacin da ake gudanar da taron wasannin Olympic na shekarar 2008. 'Game da wannan dai', cewa ya yi, ya kamata sassan kula da harkokin kiwon lafiya na birnin Beijing su yi hadingwiwa sosai tare da sashen sha'anin noma, da sashen masana'antu da kasuwanci, da sashen ilmantarwa, da sashen gine-gine, da sashen dudduba ingancin dabbobi ,da sashen zirga-zirgar jiragen sama da na jiragen kasa, da sashen zirga-zirgar motoci da kuma sashen sufuri da dai sauran sassan da abun ya shafa domin kafa wani irin cikakken tsarin bayar da labarai tsakanin sassa daban-daban da kuma na gudanar da tarurrukan hadin gwiwa tsakaninsu. Yanzu, an riga an kammala aikin kafa muhimman tsare-tsare na tsarin riga-kafi da shawo kan matsalolin kiwon lafiyar jama'a cikin hadin gwiwa.

Mun samu labarin, cewa tuni a lokacin da ake gudanar da taron dandalin tattaunawa kan hadin kan kasar Sin da Afrika a shekarar bara, gwamnatin birnin Beijing ta shirya wani gwaji daga dukkan fannoni a fannin tabbatar da ingancin kiwon lafiyar jama'a. Bisa kokarin da bangarori daban-daban suka yi tare, gwamnmatin birnin ta kammala aikin bada tabbaci ga yin jiyya a duk tsawon lokacin taron. Hakan ake sa ran alherin, cewa tsarin tabbatar da ingancin kiwon lafiyar jama'a na birnin Beijing ya cancanci a amince da shi idan an gudanar da muhimman tarurruka na kasa da kasa a birnin.

Bisa binciken da hukumar kiwon lafiya ta Beijing ta yi, an ce, a lokacin taron wasannin Olympic na Beijing, muhimman fannoni guda biyar ne da kila za su shafi matsalolin kiwon lafiyar jama'a. Fanni na farko shi ne, mugun yanayin annobar cututtuka masu yaduwa; Na biyu, shi ne matsalar samar da abinci maras inganci; Na uku, shi ne matsalar samun gurbacewar ruwan sha; Na hudu shi ne, matsalar kiwon lafiyar jama'a ta sanadiyyar samun halittu masu rai dake haddasa cututtuka; Fanni na biyar wato na karshe, shi ne sauran matsalolin ba-zata dangene da kiwon lafiyar jama'a. Game da wadannan fannoni, gwamnatin birnin Beijing ta riga tsara jerin cikakkun shirye-shirye kan yadda za a magance matsalolin ba-zata.

Mr. Liu Zejun, daraktan cibiyar shawo kan cututtuka ta birnin Beijing ya bayyana, cewa gwamnatin birnin Beijing ta rigaya ta tabbatar da matsaloli da yawansu ya kai 45, wadanda mai yiwuwa ne za su janyo illa ga taron wasannin Olympic da na nakasassu a shekarar 2008. Sa'annan ya duba yiwuwar aukuwar wadannan matsaloli da kuma hadarurrukansu. Wadannan matsaloli 45 suna kunshe da hadarurrukan annobar munanan cututtuka, da ingancin abinci da na ruwan sha da dai sauran makamantan hadarurruka da mai yiwuwa ne za su auku sakamakon yaduwar kwayoyin munanan cututtuka. ( Sani Wang )