Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-05 18:56:28    
Saukakakken tarihi na shugabannnin kasar Sin (babi na biyu)

cri

Jama'a masu sauraro,yanzu mu gabatar da Mr Wu Bangguo.Shi ne manban kwamitin dindindin na ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin kuma shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin.

An haife shi ne a watan Yuli na shekara ta 1941 a wurin Feidong na lardin Anhui,dan kabilar Han ne.A watan Afril ne na shekara ta 1964,ya shiga Jam'iyyar Kwaminis ta Sin,Ya fara aiki ne a watan Satumba na shekara ta 1966,ya gama karatunsa a sashen koyon ilimin electronics na wireless a Jami'ar Qinghua wadda ta fi shahara a kasar Sin,shi injiniya ne.

Daga shekara ta 1960 zuwa shekara ta 1967,ya yi karatu a sashen koyon ilimin wireless electroncs na jami'ar Qinghua.Daga shekara ta 1967 zuwa shekara ta 1976 yana aiki kan matsayin ma'aikaci,mallamin fasahohi,da mataimakin shugaba da shugaba na reshen kula da fasahohi na masana'antar kera electronic tubes ta uku ta birnin Shanghai.Daga shekara ta 1976 zuwa 1978,yana kan guraban mataimakin sakatare na kwamitin jam'iyyar da mataimakin shugaban kwamitin juyin juya hali da mataimakin shugaba da mataimakin sakatare na kwamitin jam'iyyar da shugaba na masana'antar kera electronic tube ta uku ta birnin Shanghai.Daga shekara ta 1978 zuwa shekara ta 1979,yana kan matsayin mataimakin manaja na kamfanin kera kayan electronics na birnin Shanghai.Daga shekara ta 1979 zuwa shekara ta 1981,yana kan matsayin mataimakin manaja na wani kamfanin electronics dabam na birnin Shanghai.Daga shekara ta 1981 zuwa shekara ta 1983 yana kan matsayin mataimakin sakatare na kwamitin jam'iyyar na hukumar kula da na'urorin aunawa da na sadarwa na birnin Beijing.Daga shekara ta 1983 zuwa shekara ta 1985,yana kan matsayin manban kwamitin dindindin na birnin Shanghai kuma sakatare na kwamitin jam'iyya mai kula da kimiyya da fasahohi.Daga shekara ta 1985 zuwa shekara ta 1991,yana kan matsayin mataimakin sakatare na kwamitin birnin Shanghai.Daga shekara ta 1991 zuwa shekara ta 1992 shi ne sakataren kwamitin birnin Shanghai.Daga shekara ta 1992 zuwa shekara ta 1994,yana kan matsayin manban ofishin siyasa na tsakiya kuma sakataren kwamitin birnin Shanghai,daga shekara ta 1994 zuwa shekara ta 1995,yana kan matsayin manban ofishin siyasa na tsakiya kuma sakataren sashen sakatariya na tsakiya.Daga shekara ta 1995 zuwa shekara ta 1997,yana kan matsayin manban ofishin siyasa na tsakiya,kuma sakatare na sashen sakatariya na tsakiya da mataimakin firayim minista na kasar Sin.Daga shekara ta 1997 zuwa shekara ta 1998,yana kan matsayin manban ofishin siyasa na tsakiya kuma mataimakin firayim minista na kasar Sin.Daga shekara ta 1998 zuwa shekara ta 1999,yana kan matsayin mamban ofishin siyasa na tsakiya kuma mataimakin firayim minista da sakataren kwamitin aiki na tsakiya mai kula da manyan masana'antu.Daga shekara ta 1999 zuwa shekara ta 2002,yana kan matsayin ofishin siyasa na tsakiya da mataimakin firayim minista da dan kungiyar jam'iyyar kuma sakataren kwamitin aiki na tsakiya mai kula da masana'antu. A shekara ta 2002,yana kan matsayin manban ofishin siyasa na tsakiya kuma mataimakin firayim minista da dan kungiyar jam'iyyar kuma sakataren kwmitin aiki na tsakiya mai kula da masana'antu.A gun cikakken zama na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da aka yi a watan Maris na shekara ta 2003 aka zabe shi da ya zama shugaban kwamitin dindindin na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin.

Mr Wu Bangguo mamba na ba cikakke ba na kwamitin tsakiya 12 da na 13 na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta Sin,manban kwamitin tsakiya da manban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya,An kara shi a sashen sakatariya na kwamitin tsakiya a matsayin sakatare a cikakken zama na hudu na kwamitin tsakiya na 14,shi kuma manban kwamitin tsakiya da manban ofishin siyasa na tsakiya na kwamitin tsakiya na 15 da 16.aka zabe shi da ya zama manba na kwamitin dindindin na ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na 16.

Jama'a masu sauraro,wannan shi ya kawo karshen saukakken tarihi na shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Mr Wu Bangguo,to sai ku cigaba da sauraron shirye-shiryenmu.