Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-04 19:06:04    
Wani mai yin nazari kan sana'ar yin kayayyakin al'adu na kasar Sin mai suna Jin Yuanpu

cri

Shehun malami Jin Yuanpu mai shekaru 56 da haihuwa shi ne wani mashahurin masani a fannin yin nazari kan sana'ar yin kayayyakin al'adu na kasar Sin. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, ya yi kokarin yin nazari kan damar da wasanin Olimpic na shekarar 2008 za su samar wa masana'antun yin kayayyakin al'adu na kasar Sin, saboda haka ya ba da tasiri sosai wajen rukunonin masu fasaha da na masana'antu.

Mr Jin Yuanpu shi ne wani shehun malami na fannin yin nazari kan ka'idoji da manufofi na yau da kullum na bayyana abubuwa masu kyaun gani wajen halittu da zamantkewar al'umma da fasahohi ta hanyar kimiyya. Tun daga shekaru 90 na karnin da ya gabata, bisa albarkacin raya masana'antun yin kayayyakin al'adu a kasar Sin, Mr Jin Yuanpu ya soma mai da hankali ga yin nazari kan masana'natun yin kayayyakin al'adu, yana daya daga cikin rukunin farko na masanan da suka soma bayyana wa hasashen sana'ar yin kayayyakin al'adu da aiwatar da shi, sa'anan kuma ya zama shugaban ofishin yin nazari kan sabbin kayayyakin al'adu na jami'ar jama'ar kasar Sin, kuma shi ne ya soma yin nazari kan halayen musamman na sana'ar yin kayayyakin al'adu na kasar Sin da sauran batutuwa, ya bayyana cewa, lokacin da na soma bayyana wa kasar Sin ilmi dangane da abubuwa masu kyaun gani, na fahimci cewa, mutanen kasashen yamma sun mai da hankali ga dangantakar da ke tsakanin ilmin da jama'a suke da su wajen raya abubuwa masu kyaun gani da al'adu masu yaduwa a ko'ina, a farkon shekaru 90 na karnin da ya gabata, kasar Sin ta soma raya sana'ar yin kayayyakin al'adu, sa'anan kuma na soma yin nazari kan al'adun jama'a, ya zuwa yanzu na soma mai da hankali ga yin nazari kan sana'ar yin kayayyakin al'adu da kuma bayyana wa kasar Sin sana'ar yin sabbin kayayyakin al'adu na kasashen waje.

A ganin Mr Jin Yuanpu, gasar wasannin Olimpic gasa ce da duk duniya ta zura ido a kai, ma'anar gasar ba ta nuna a wajen wasannin motsa jiki kawai ba. Sai ya gabatar da wani ra'ayi da ke cewar " In duniya ta ba ni kwanaki 16, to dole ne zan mayar wa duk duniya shekaru dubu 5, Mr Jin Yuanpu ya bayyana cewa, a ganina, a gaskiya dai wasannin Olimpic sun samar wa birnin Beijing wani sarari mai kyau, sai mu ce, duniya ta samar mana kwanaki 16, kuma mu mayar wa duniya shekaru dubu 5, muhimmin burin nan shi ne don bayyana al'adun kasar Sin da ke da wadatattun abubuwa, kuma ta hanyar wasannin Olimpic ne za a bayyana Beijing da ke da al'adu da Beijing da ke fitar da sabbin kayayyakin al'adu da sabuwar fuskar Beijing, sa'anan kuma, ta hanyar wasannin Olimpic da za a yi a birnin Beijing ne mutanen kasashen waje za su bayyana al'adunsu a Beijing.

Ra'ayin nan ya sami goyon baya daga wajen gwamnatin birnin Beijing. Kuma ra'ayoyinsa da yawa su ma sun sami amincewa daga wajen sassan da abin ya shafa na gwamnatin Beijing, wannan ya sa Mr Jin Yuanpu ya yi farin ciki sosai da sosai.

Daga shekarar 2003, hukumar Mr Jin Yuanpu ta shirya tarurukan tattaunawa a tsakanin kasa da kasa kan batun wasannin Olimpic har shekaru hudu a jere, kuma ta gayyaci kwararru da masana na kasashen waje da su gabatar da shawararsu kan wasannin Olimpic na shekarar 2008. A wajen Mr Jin Yuanpu, aikin nan shi ne dama mai kyau da kasar Sin ta samu wajen bayyana ainihin abubuwan al'adun kasar Sin da kuma koyon al'adun kasashen waje.

A sa'I daya kuma Mr Jin Yuanpu ya gano wasu matsalolin da aka samu, ya bayyana cewa, kodayake ana mai da hankali sosai da sosai a kan sana'ar yin kayayyakin al'adu a kasar Sin, amma ya kamata a fahimci cewa, kasar Sin kasa ce da take mai da hankali ga raya masana'antun kere-kere, sa'anan kuma ta mai da hankali sosai ga sauran masana'antu da dai sauran irinsu. Wajen aikin samar da hidima, ya kamata a sami abun da ke dace da tsarin raya sana'ar yin kayayyakin al'adu.

Ayyukan yau da kullum na da yawan gaske ga Mr Jin Yuanpu , amma in ya sami dan lokacin hutu, sai ya shiga aikin internet, ya rubuta bayanai a kan ilmi dangane da abubuwa masu kyaun gani da dai sauransu.(Halima)