Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-04 18:38:24    
Jarumin wasan tsalle-tsalle da guje-guje na Kenya yana matukar kaunar kasar Sin

cri
Shi ne daya daga cikin mashahuran da suka yi suna a fagen wasan tsalle-tsalle da guje-guje a Afirka, an mayar da shi tamkar 'baban wasan gudu na dogo da matsakaicin zango na kasar Kenya'. Yana shugabantar kwamitin wasan Olympic na Kenya, shi ne kuma mamba kawai na Kenya da ke cikin kwamitin wasan Olympic na kasa da kasa. Yana himmantuwa kan sha'anonin jin dadin jama'a, ya samar wa marayu kusan 500 damar samun ilmi, ya kuma kafa cibiyar horaswa ta wasan tsalle-tsalle da guje-guje don samar wa Kenya mahaifiyarsa kwararru. Tun da farko har zuwa karshe ya tsaya tsayin daka kan bai wa kasar Sin goyon baya wajen neman samun damar shirya taron wasanninn Olympic na shekara ta 2000 da ta 2008, ya kuma sa kaimi kan sauran mambobin kwamitin wasan Olympic na duniya da suka zo daga kasashen Afirka da su goyi bayan kasar Sin.

Shi ne shahararren dan wasa a fagen wasan tsalle-tsalle da guje-guje na duniya, sunansa Kipchoge Keino. Ran 27 ga watan jiya rana ce da ya rage sauran kwanaki 500 da soma taron wasannin Olympic na Beijing, a ran 26 ga watan jiya, bisa agogon wurin, Mr. Keino ya zanta da wakilinmu cikin farin ciki.

A matsayinsa na mamban kwamitin wasan Olympic na kasa da kasa da kuma mamban kwamitin kula da dukkan ayyuka na taron wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008, Mr. Keino ya sha ziyarar kasar Sin, musamman ma a shekarun baya da suka wuce, ya kai ziyara a birnin Beijing sau 2 a ko wace shekara, inda ya kan dudduba ayyukan gina filayen wasa da kasafin kudi da zirga-zirga da bunkasuwar kasuwanni da dai sauransu. A watan Nuwamba na shekarar bara Mr. Keino ya sake zuwa Beijing, ya gano sauye-sauye da yawa da Beijing ya samu bisa na watanni da dama da suka wuce, ya ce,'Mun gano sauye-sauye da yawa a Beijing, an dasa bishiyoyi da ciyayi a kewayen filayen wasa da ke jami'o'i, muna farin ciki saboda dalibai za su yi amfani da wadannan filayen wasa bayan taron wasannin Olympic. Bayan hakan kuma, Beijing yana shimfida hanyoyi da samar da hanyoyin jiragen kasa da ke karkashin kasa da kuma kyautata muhalli, shi ya sa Beijing zai zama wuri mai kyau wajen yin taron wasannin Olympic.'

Saboda ganin halin da Beijing ke ciki wajen shirya taron wasannin Olympic na shekarar 2008, Mr. Keino ya nuna aniya sosai kan cin nasarar yin taron wasannin Olympic na Beijing. Ya ce,'Na yi imanin cewa, tabbas ne taron wasannin Olympic na Beijing zai zama taron wasannin Olympic ne mafi cin nasara a tarihi. Na ji an ce, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing yana namijin kokari ba tare da kasala ba don tabbatar da cin nasarar shirya taron wasannin Olympic a shekara mai zuwa. Mun ji alfarma saboda ganin cewa, dukkan gwamnatin Sin da jama'arta sun hada kansu suna yin kokari tare. Sa'an nan kuma, na sami damar kallon taron wasannin motsa jiki na duk kasar Sin, inda 'yan wasa na larduna daban daban na kasar suka yi takara tare, kwarewarsu na da kyau sosai, a ganina, hakan wani bangare ne na ayyukan shiryawa, shi ya sa, yanzu na iya tabbatar da cewa, a shekara mai zuwa, kasar Sin za ta nuna mana wani taron wasannin Olympic da ba safai a kan ga irinsa ba.'

Tun farko har zuwa karshe Mr. Keino yana tsayawa tsayin daka kan bai wa kasar Sin goyon baya a fannin neman samun damar shirya taron wasannin Olympic na shekara ta 2000 da ta 2008, ya kuma dauki matakai don sa kaimi kan takwarorinsa na kwamitin wasan Olympic na duniya da suka zo daga sauran kasashen Afirka da su goyi bayan kasar Sin da ta sami damar shirya taron wasannin Olympic.

Game da dalilin da ya sa hakan, Mr. Keino yana ganin cewa, dalilin shi ne domin mutanen Sin sun burge shi sosai. Ya ce,'A lokacin da birnin Sydney ya lashe Beijing, ya sami damar shirya taron wasannin Olympic na shekarar 2000, mutanen Sin sun yi kuka, na gano cewa, mutanen Sin na alla-allar samun damar shirya taron wasannin Olympic. Tun daga lokacin can na fara mai da hankali kan kasar Sin, na kuma shawo kan abokaina da su kada kuri' a tare da ni, saboda ya kamata kasar Sin ta sami wannan dama mai daraja. Ko shakka babu, kamata ya yi ko wace kasa ta iya samun wannan dama, amma a cikin tarihinta, kasar Sin ba ta taba shirya taron wasannin Olympic ba tukuna, shi ya sa ina ganin cewa, bai wa kasar Sin damar shirya taron wasannin Olympic ya kasance tamkar girmamawa ce da aka bai wa gwamnatin Sin da jama'ar Sin da kuma matasan Sin, a lokacin nan, za mu yi takara da kuma samun sabbin abokai tare a kasar Sin, abu mafi muhimmanci shi ne mu ne aminai a yanzu, muna koyi da juna.'

A lokacin kuruciyarsa, Mr.Keino ya ci nasara da yawa, yanzu ya tsufa, amma yana sadaukar da ransa ga Kenya mahaifiyarsa a matsayin shugaban kwamitin wasan Olympic na Kenya. A sa'i daya kuma, yana kaunar kasar Sin a cikin zuciyarsa. Yana fatan Sinawa masu yawa, musamman ma matasa za su shiga wasannin motsa jiki. Ya kuma yi alfahari da gwamnatin Sin da jama'arta saboda suna bai wa kasashe marasa ci gaba taimako, musamman ma ga Kenya. A idon Mr. Keino, mutanen Sin da mutanen Kenya su aminai ne, ya kamata su ci gaba da dankon zumuncin da ke tsakaninsu.(Tasallah)