Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-04 14:50:31    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(29/03-04/04)

cri
Ran 27 ga watan Maris, a nan Beijing, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya kaddamar da kasafin lambobin yabo na taron wasannin Olympic na lokacin zafi na karo na 29 a hukunce. Bambanci mafi girma a tsakanin wadannan lambobin yabo da wadanda aka yi amfani da su a da shi ne an sa lu'ulu'u irin na Jade a bayan wadannan lambobin yabo. An fito da wannan shiri ne a karo na farko a tarihin wasannin Olympic mai tsawon shekaru 100 ko fiye.

Akwai wani labari daban daga kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing, an ce, a ran 28 ga watan Maris, an fara daukar masu aikin sa kai don gasannin taron wasannin Olympic na Beijing da na nakasassu daga 'yan uwanmu na yankunan musamman na Hongkong da Macao da lardin Taiwan da Sinawa 'yan kaka gida da kuma mutanen kasashen waje. Ban da wannan kuma, a wannan rana, mataimakin shugaba mai zartaswa na wannan kwamiti Mr. Li Binghua ya fayyace cewa, tun daga ran 28 ga watan Agusta na shekarar bara da aka fara daukar masu aikin sa kai har zuwa yanzu, mutane fiye da dubu 410 sun yi rajistar neman zama masu aikin sa kai domin gasannin taron wasannin Olympic na Beijing da na nakasassu. Za a tabbatar da irin wadannan masu aikin sa kai na rukuni na farko kafin watan Agusta na wannan shekara.

Ran 1 ga watan Afril, a birnin Melbourne na kasar Australia, an rufe gasar fid da gwani ta wasan iyo ta duniya a karo na 12. Kungiyar kasar Sin ta sami lambobin zinariya 9 a cikin gasannin tsinduma cikin ruwa, ta haka ta zama ta 3 tare da kungiyar kasar Australia a cikin jerin kasashen duniya a fannin samun lambobin zinariya. Kasar Amurka ta zama ta farko, kasar Rasha ta zama ta biyu a wannan karo.

Ran 30 ga watan Maris, hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta duniya wato FIFA ta sanar da cewa, har zuwa yanzu, kungiyoyi 204 na wasan kwallon kafa sun yi rajista za su shiga gasannin zagaye na farko don tace gwanayen da za su shiga gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa da za a yi a shekara ta 2010, yawan kungiyoyin ya karya matsayin bajimta a tarihin wannan muhimmiyar gasar wasan kwallon kafa. Yanzu sai kasashen Philippines da Bhutan da Laos da Brunei kawai ba su yi rajista ba tukuna. Za a fara yin gasannin zagaye na farko don tace gwanayen da za su shiga gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta shekara ta 2010 a watan Agusta na wannan shekara.(Tasallah)