Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-03 21:10:38    
Mutane suna damuwa da halin da ake ciki a kasar Somaliya

cri

A ranar 2 ga wannan wata , gwamnatin rikon kwarya ta kasar Somaliya ta kirayi mutanen da ke zama a birnin Mogadishu, hedkwatar kasar da su tashi daga gidajensu kafin farmakin soja na sabon karo da za a yi. Wannan ya bayyana cewa, za a ci gaba da kazamin fada wanda ake yi ta yi cikin kwanaki hudu a birnin Mogadishu a tsakanin sojojin gwamnatin rikon kwarya da na Habasha da dakarun kabilar Hawiye na Somaliya. Wannan ya sa mutane suna kara nuna damuwarsu a kan bunkauwar lalacewar halin tsaro da ake ciki a kasar Somaliya.

A wannan rana, mataimakin ministan tsaron kasa na gwamnatin rikon kwarya ta Somaliya Mr Salad Ali Jelle ya bayyana cewa, a ranar 1 ga wannan wata, dakarun kabilar Hawiye sun sanar da cewa, yarjejeniyar dakatar da wutar yaki a duk fadin birnin Mogadishu da suka daddale tare da sojojin kasar Habasha takarda ce ta wofi. Ya ce, a cikin kwanaki hudu da suka wuce, sojojin gwamnatin rikon kwarya na kasar Somaliya da sojojin kasar Habasha sun yi kazamin fada da 'yan ta'adda tare. Ya kai suka cewa, dakarun da suka yi kazamin fada da sojojin gwamnatin rikon kwarya da na Habasha suna da nasaba da kungiyar Al Qaida, Mr Jelle ya kuma nemi wasu mazaunan da ke zama cikin birnin Magadishu da su tashi daga birnin tun da wuri, saboda sojojin gwamnatin rikon kwarya za su ga damar kai sabon farmaki kan 'yan ta'adda da ke da zama  a wadannan wurare.

Daga ranar 29 ga watan Maris, sojojin gwamnatin rikon kwarya na kasar Somaliya da na kasar Habasha sun tura tankoki da jiargen sama masu saukar ungulu don kai babban farmaki kan inda dakarun kabilar Hawiye suke da zama a cikin birnin Mogadishu . Kungiyar Red Cross ta kasashen duniya ta bayyana cewa, wannan ne yaki mafi tsanani da aka yi a birnin Mogadishu tun daga shekarar 1991 da kasar Somaliya ta rasa tsayayyar gwamnati har zuwa yanzu, bisa kwarya kwaryar kididdigar da aka yi, an ce, a cikin kazamin yaki da aka yi cikin kwanaki hudu, mutane 381 sun mutu a yayin da mutane 565 suka ji raunuka, yawancinsu jama'ar farar hula ne. Don gudun wutar yaki, mazaunan Mogadishu bi da bi ne suka gudu daga gidajensu. Bisa sanarwar ofishin hukumar 'yan gudun hijira na Majalisar dinkin duniya , an bayyana cewa, a cikin kwanaki goma da suka wuce kawai, yawan mutanen da suka gudu daga birnin Mogadishu ya kai dubu 47, saboda haka, yawan mutane da suka gudu daga gidacjensu bisa sakamakon hargitsin yakin ya kai dubu dari a cikin watanni biyu.

A gaskiya dai ne, a kwanan baya, yakin nan ba na karo na farko ba ne da aka yi a tsakanin sojojin gwamnatin rikon kwarya da na Habasha da dakaru kabilar Hawiye, a tsakiyar watan Maris,bangarorin biyu sun taba yin kazamin yaki a tsakaninsu, kabilar Hawiye tana daya daga cikin mnayan kabilun da ke kudu maso tsakiyar kasar Somaliya, kuma kabila ce da ke da karfi sosai a birnin Mogadishu, kabilar tana nuna rashin gamsuwarta ga gwamnatin rikon kwarya tun daga farko har zuwa yanzu, ana ganin cewa, wani bangaren kabilar tana nuna goyon baya a boye ga aikin ta'addanci da kungiyar Al Qaida take yi.

Tun daga shekarar 1990 har zuwa yanzu, kasar Somaliya tana cikin halin rashin tsayayyar gwamnati. A karshen shekarar da ta gabata, bisa taimakon sojojin kasar Habasha ne, gwamnatin rikon kwarya da aka riga aka kafa ta cikin shekaru da yawa kuma ba ta da karfin shiga cikin hedkwatar kasar ta kwace ikon mallakar yawancin wuraren kasar ciki har da birnin Mogadishu, amma tun daga watan Maris na shekarar da muke ciki, musamman ma bayan da majalisar wucin gadi ta kasar Somaliya ta zartas da kuduri na maida gwamnatin rikon kwarya daga Baidoa zuwa Mogadishu a ranar 12 ga watan Maris, sai birnin Mogadishu ya yi ta shiga cikin al'amuran haddasa farmaki da aka yi.

Bayan kazamin fada da aka yi cikin kwanaki hudu, a ranar 1 ga watan Afril, kabilar Hawiye ta sanar da cewa, za a dakatar da aikin nuna adawa da juna a birnin Mogadishu daga wannan rana da karfe biyu na yamma. Kodayake sanarwar ta kawo wa Mogadishu fatan haske, amma manazartan al'amarin sun bayyana cewa, ba a iya sa ran alheri ga halin da ake ciki a birnin Mogadishu ba, Bisa halin nan ne za a ci gaba da sa ido kan al'amarin nan.(Halima)