Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-03 19:07:56    
Tashar jiragen ruwa na Wusongkou ta Shanghai

cri

Salamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin, wanda mu kan gabatar muku a ko wace ranar Talata. Kamar yadda muka saba yi, da farko dai, za mu karanta muku wasu abubuwa kan wata shahararriyar tashar jiragen ruwa da ke birnin Shanghai, sunanta Wusongkou, daga baya kuma, sai wani bayanin musamman mai lakabi haka 'Yin ziyara a lardin Sichuan', wanda yake kudu maso yammacin kasar Sin.

Tashar jiragen ruwa ta Wusongkou da ke bakin kogin Huangpijiang an fara aiki da ita ne a shekara ta 2003 a matsayin tashar jiragen ruwa ta Shanghai mai karbar fasinjoji na gida, ta maye gurbin tashar jiragen ruwa ta Shiliupu da ke kan titin Waitan, wadda aka yi shekaru fiye da 130 ana amfani da ita. Gina tashar jiragen ruwa ta Wusongkou wani muhimmin bangare ne na shirin raya birnin Shanghai a cikin sabon karni. An gina wannan tashar jiragen ruwa ne don canza kogin Huangpujiang zuwa wani kogin kasa. A can da kogin Huangpujiang ya taka rawa sosai a fannin raya masana'antu, amma nan gaba yana iya samar wa 'yan birnin Shanghai kyawawan wurare masu ni'ima.

An yi amfani da kudin Sin misalin yuan miliyan dari 2 wajen gina wannan tashar jiragen ruwa mai fadin kadada 24.5 bisa gabar kogi mai tsawon misalin mita 700, wadda ke da hannun kogi mai zurfin misalin mita 11.

Tashar jiragen ruwa na Wusongkou ya dace da sufuri da harkokin ciniki da kuma abubuwan nishadi. Wata hasumiya mai tsawon misalin mita 180 da aka yi da bakin karfe ta zama alama ce ga wannan tashar jiragen ruwa, masu yawon shakatawa na iya daukar lif don more idanunsu da ni'imtattun wurare da ke bakin kogin a dandamali mai tsawon mita 120 daga doron kasa.

Saboda tashar jiragen ruwa tana daukar nauyin jigilar fasinjoji da kayayyaki na gida, shi ya sa aka mayar da ita a matsayin kofa ta birnin Shanghai daga ruwa da kuma cibiyar sufuri. Tashar jiragen ruwan nan ta kuma ba da gudummowa wajen raya arewacin birnin. Jiraren ruwa suna kaiwa da dawowa a kan lokaci kamar yadda aka tsara a tsakanin tashar jiragen ruwa ta Wusongkou da birnin Dalian na lardin Liaoning da tsibirin Zhoushan da ke kunshe da kananan tsibirai na lardin Zhejiang da kananan tsibirai 3 na Shanghai wato Chongming da Changxing de Hengsha, da kuma wasu biranen da ke gabar kogin Yangtze. Mutanen da suka sauka tashar jiragen ruwa ta Wusongkou suna iya zuwa lardin Zhejiang da ke makwabtaka da birnin Shanghai cikin motoci, haka kuma suna iya zuwa lardunan Jiangsu da Anhui cikin motoci na dogon zango.