Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-03 19:02:28    
Gidan ibada na Xuankongsi, wani ginin da aka gina a sararin sama

cri

An gina gidan ibada na Xuankongsi a cikin wani kwari na gundumar Hunyuan a shekara ta 491, wato ke nan yau da shekaru fiye da 1500 da suka wuce. An yi wannan gini ne a jikin rabin dutse, yana da nisan mita misalin 50 a tsakaninsa da doron kasa, yana kasancewa kamar an hada shi a kan kwazazzabo, kwazazzabon da shi sun zama abu daya. Saboda an gina shi a cikin wata gangarar da ke jikin rabin dutsen, shi ya sa ya iya kasucewa ruwan sama da hasken rana a ko wane lokaci, ko bayan shekaru dubu dubai, har zuwa yanzu an rataye shi a kan kwazazzabon sosai da sosai.

Gidan ibada na Xuankongsi wani gini ne da aka yi a katako, kuma fadinsa ya kai murabba'in mita 152.5 kawai, ya hada da dakuna manya da kanana 40. In an hange shi daga nisa, ginshikan katako gomai suna daure wa wadannan manyan fadoji da dakuna gindi, sa'an nan kuma, wani katon dutse da ke samansa yana kasancewa kamar yadda yake sauka kan gidan ibada na Xuankongsi.

Masu yawon shakatawa da suka zo nan ziyara dukkansu sun darajanta sosai kan wannan gini. An shimfida hanyoyin katako marasa fadi a tsakanin ko wane daki na gidan ibada na Xuankongsi. Wadannan hanyoyin katako na iya daukar mutum daya kawai a ko wane karo. Da zarar mutane sun kama wadannan hanyoyi, sai sun yi dagyaldagyal, sun ja numfashi, sun mai da hankulansu sosai da sosai a lokacin da suke sa kafa a kan katakon, suna tsoron dukkan gidan ibada na Xuankongsi zai ruguje a sakamakon kuskurensu.

Masu yawon shakatawa su kan yi tsammani cewa, ginshikai na katako guda 30 da ke karkashin gidan ibadan su ne suke daure gindinsa a lokacin da suke ziyara a nan a karo na farko. Amma malam Sun Yi, wanda ke nazarin gidan ibada na Xuankongsi, ya musunta ra'ayi mai kamar haka, ya yi bayani cewa, 'Sigar musamman mafi girma da gidan ibada na Xuankongsi ke da ita ita ce, a gaskiya, dukkan wadannan ginshikai ba su ne suke daukar nauyin gidan ibadan ba, a maimakon haka, an sossoka katakai masu yawa a jere da suka ratsa jikin dutsen, kuma a kan katakan ne aka gina wannan gidan ibada mai suna Xuankongsi.'

Irin wadannan katakai da malam Sun ya ambata su 27 ne, wadanda suke kasancewa kamar wani bangare ne na jikin dutsen. Katakan na daukar dukkan nauyin dakin ibada na Xuankongsi. Malam Sun ya kara da cewa, wasu daga cikinsu na daukar nauyi, wasu kuma suna shawo kan daidaituwar wannan babban gini.

Malam Luo Zhewen, wani masani ne mai ilmin tsoffin gine-gine na hukumar kula da kayayyakin gargajiya ta kasar Sin, ya yi shekaru fiye da 20 yana nazarin gidan ibada na Xuankongsi, a ganinsa, an gina wannan gini mai ban mamaki ne ta hanyar da tsuntsaye ke bi wajen gina shekuna, ya ce, 'Yana kasancewa da kananan tuddai ko kuma kwaruruka a kan babban dutsen, an hada su ta hanyar yin amfani da katako ko kuma gadoji, ta haka an sami wani wuri, wanda ke kasancewa ikon Allah, yana da daraja sosai ta fuskar fasaha.'

Babbar sigar musamman ta gidan ibada na Xuankongsi ita ce a lokacin da ake gina shi, an yi la'akari da wurin da yake zaune, an gina dukkan rassansa bisa yadda canjin kwazazzabon yake.

Kazalika kuma, gidan ibada na Xuankongsi gidan ibada ne kurum inda ake bauta wa addinan Buddha da Tao da kuma Confucius tare. A gaskiya kuma, addinin Confucius ba wani addini ba ne, amma mutanen Sin sun bauta masa a matsayin addini. A cikin babbar fada mafi tsayi a nan, an ajiye mutum-mutumin Sakyamuni da Lao-tzu da kuma Confucius tare. Tsohon shugaba na farko na ofishin kula da gidan ibada na Xuankongsi malam Zhang Jianyang ya bayyana cewa, 'Masu yawon shakatawa na gida da na waje sun kai ziyara ga gidan ibada na Xuankongsi, sa'an nan kuma dukkansu sun ziyarci wannan babbar fada da aka ajiye mutum-mutumin wadannan shugabannin addinai 3 tare, kasar Sin ita kasa ce kawai da aka ajiye mutum-mutumin shugabannin addinai 3 tare, ta nuna ra'ayi mai kyau.'

Masu sauraro, yanzu mutane kimanin dubu goma su kan kai wa gidan ibada na Xuankongsi ziyara a ko wace rana. Ni'imtattun wurare da ba a ganin iri-irinsu a sauran wurare da kuma fasahar gine-gine mai ban mamaki sun sanya masu yawon shakatawa na gida da na waje su ji mamaki sosai. Idan kuna sha'awar wannan gidan ibada, to, muna maraba da ku zuwa birnin Datong na lardin Shanxi don ziyarar shi.