Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-03 18:53:52    
Maganin rage zafin haihuwa zai iya yin illa ga nonon iyaye mata

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku wani bayani kan cewa, maganin rage zafin haihuwa zai iya yin illa ga nonon iyaye mata, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani kan tsarin daidaita matsalolin da za su iya faruwa ba zato ba tsammani a birane. To, yanzu ga bayanin. Wani binciken da kasar Australia ta gudanar ba da jimawa ba ya bayyana cewa, mai yiyuwa ne maganin rage zafin haihuwa zai yi illa ga nonon iyaye mata.

Bisa labarin da muka samu daga tashar Internetr ta mujallar "Sabbin masu ilmin kimiyya", an ce, manazarta na jami'ar Sydney ta kasar Australia sun gudanar da wani bincike ga mata 416 da aka yi musu allurar maganin rage zafin haihuwa lokacin da suke haihuwa da mata 312 da ba su sha irin wannan magani ba. Kuma sakamako ya gano cewa, game da matan da aka yi musu allurar maganin rage zafin haihuwa a cikin lakarsu da ke kashin baya, yiyuwar daina samar da nono lokacin da shekarun yaransu ya kai watanni shida ta ninka guda idan an kwatanta da wadanda ba su sha irin wannan magani ba.

Yin allura a cikin lakar da ke kashin baya tana daga daga cikin hanyoyin iri daban daban da a kan bi da ke wajen rage zafin haihuwa. Kuma manazarta sun bayyana cewa, ya zuwa yanzu ba su gano cewa, ko maganin rage zafin haihuwa yana iya yin illa ga jarirai wajen shan nono, ko ga mata wajen samar da nono, shi ya sa ake bukatar ci gaba da yin nazari a kan shi.

Amma wani binciken da aka gudanar a da ya bayyana cewa, jariran da iyayensu mata suka sha maganin rage zafin haihuwa a lokacin haihuwa sun fi yawan barci idan an kwatanta su da wadanda iyayensu mata ba su sha maganin rage zafin haihuwa ba. Sabo da haka mai yiyuwa ne wannan zai iya yin illa ga jarirai wajen shan nono. yanzu za mu ba ku wani labari daban game da shan nonon iyaye mata. Bisa wani sabon nazarin da kasar Amurka ta yi, an ce, shan nonon iyaye mata zai iya kayyade yawan kwayar halitta wadda ake kiranta "Gene" a bakin turawa, ta haka za a ba da taimako ga jarirai wajen hana kamuwa da cuttuttuka kunnuwa.

Manazarta na sashen ilmin likitanci na jami'ar Texas ta kasar Amurka sun tattara kwayoyin halitta na yara 505 na jihoyin Texas da Kentucky, kuma an tabbatar da cewa, kashi 60 cikin dari daga cikinsu sun fi saukin kamuwa da cuttuttukan kunne. Manazarta sun yi nazari kan karamin bambanci tsakanin kwayoyin halitta iri na 3 wadanda ke da nasaba da kumburi.

Daga baya kuma an gano cewa, kwayoyin halitta iri na biyu da ke cikinsu suna da nasaba da cuttuttukan kunne, amma idan jarirai sun sha nonon iyaye mata, to za a iya dakushe illar da su kan yi, ta haka za a iya kara karfin garkuwar jiki.