Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-02 16:56:13    
Ayyukan jiyya na unguwannin birnin Beijing

cri

A yammacin birnin Beijing, akwai wata unguwa wadda ake kiranta "Yongle", inda wakilinmu ya gamu da Madam Li da shekarunta ya kai kusan 70 da haihuwa. A lokacin da, idan ta kamu da cututtuka, ta kan je wani babban asibitin da ke tsakiyar birnin Beijing domin ganin likita. Ba kawai tana kwashe lokaci da yawa wajen zuwan wurin ba, har ma muhallin ganin likita na asibitin ba shi da kyau. Kuma Madam Li ta gaya mana cewa, "Ana iya samun mutane da matukar yawa wajen ganin likita a wancan babban asibiti, shi ya sa ba na son zuwan can."

Haka kuma ta kara da cewa, ta kamu da cutar kashi da ake kiranta "hyperosteogeny", tana bukatar zuwan asibiti har sau biyu ko uku a ko wane wata, amma yanzu ba za ta je babban asibitin da ke tsakiyar birnin Beijing domin ganin likita ba, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da abisitin Shijingshan da ke kusa da unguwar da Madam Li take zama ya kafa wata cibiyar jiyya a unguwar, za a iya yin mata jiyya a tashar. Ban da wannan kuma idan cutarta ta tsananata, cibiyar jiyya ta unguwar za ta tura mota wajen dauka ta zuwa asibitin Shijingshan domin ci gaba da yin mata jiyya.

Sunan shugaban cibiyar jiyya ta unguwar Longle shi ne Yu Guihua. Kuma ta gaya wa wakilinmu cewa, yanzu ana iya samun yawancin kayan aikin jiyya na kasar Sin a birane, amma ana iya samun mutane mafi yawa a kauyuka. Sabo da haka idan mutane sun kamu da cututtuka, su kan je birane domin ganin likita, kuma wannan shi ne wani muhimmin dalili da ya sa yana da wuya wajen ganin likita a manyan asibitoci. A waje daya kuma, game da mazaunan birane, idan sun kamu da cututtuka, su kan zabi zuwan manyan asibitoci don ganin likita a maimakon zuwan asibitoci kanana da matsakaici, wannan ya haddasa kasancewar rashin daidaito wajen yin amfani da albarkatun jiyya.

Ban da wannan kuma Madam Yu ta ce, cibiyoyi jiyya da birnin Beijing yake kafawa a unguwanni suna iya warkar da cututtukan da mazauna su kan kamu da su kamar mura da gudawa da raunuka marasa tsanani da dai sauransu. Ta haka za a iya rage yawan lokacin da wadanda suka kamu da cututtuka suke kwashewa a kan hanya wajen ganin likita, a waje daya kuma za a iya sassauta nauyin da ke bisa wuyan manyan asibitoci. Kuma Madam Yu ta kara da cewa, "Akwai likitoci biyu a cibiyar jiyya ta unguwarmu, amma suna iya warkar da mutanen da suka kamu da cututtuka maras tsanani. Idan mutane sun zo tashar domin ganin likita, sai a bude na'urar kwamfuta, shi ke nan, za a iya ganin halin cututtukan da suke ciki, da kuma magungunan da su kan sha. Shi ya sa akwai sauki gare mu wajen yi musu jiyya."

Bugu da kari kuma Madam Yu ta bayyana cewa, ya fi sauki ga wadanda suka zo cibiyar jiyya ta unguwar Yongle don ganin likita idan an kwatanta da manyan asibitoci. Kuma ta ce, "Masu fama da cututtuka sun zo tasharmu su ganin likita da farko, daga baya kuma su biya kudin ragista wajan ganin likita, sabo da haka an samar da sauki ga tsofaffi. Idan muna son jawo hankulan mutane, ba yadda za a yi sai mu tafiyar da kyawawan ayyukan ba da hidima. Idan masu fama da cututtuka ba su iya zuwan cibiyarmu ba, muddin su buga mana wayar tarho, sai za mu isa gidajensu a cikin mintoci biyar."

Bayan da kafuwar cibiyoyin jiyya ta unguwanni, yanzu ba za a bukaci a kwashe lokaci da yawa wajen zuwan manyan asibitoci don ganin likita ba. Amma akwai wata matsala daban da ke damuwar mazaunan Beijing wadanda albashinsu bai taka kara ya karya ba, wato magunguna suna da tsada. Domin warware matsalar, gwamnatin birnin Beijing ta riga ta dauki matakai.

Yau da watanni biyu da suka gabata, birnin Beijing yana jagorantar tafiyar da ayyukan sayar da magunguna ba tare da neman riba a hukumomi fiye da 2600 na ba da hidima kan kiwon lafiya na unguwanni, kuma cibiyar jiyya ta unguwar Yongle tana daya daga cikinsu.

Madam Yu ta gaya mana cewa, bayan da aka fitar da wannan sabuwar manufa, yawan kudaden ganin likita ya samu raguwa sosai, haka kuma yawan mutanen da suka zo tashar domin ganin likita ya karu sosai.

Game da wadannan matsalolin biyu, wato ganin likita yana da wuya da kuma ganin likita yana da tsada, gwamnatin kasar Sin ta fitar da manufofi da yawa domin warware su, kamar yadda firayin minista Wen Jiabao na kasar Sin ya yi alkawari a cikin rahoton aikin gwamnatin kasar, "Ya kamata a gaggata kafa tsarin ba da hidima wajen kiwon lafiya na birane irin na sabon salo bisa tushen unguwanni, kuma kamata ya yi a mai da hankali kan raya ayyyukan ba da hidima na kiwon lafiya na unguwanni, ta yadda za a ba da sauki ga fararen hula wajen shawo kan cututtuka." Kande Gao)