Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-02 16:55:05    
Takaitaccen bayani game da kabilar Qiang

cri

Yawancin 'yan kabilar Qiang na kasar Sin suna zama ne a gundumar Maowen ta kabilar Qiang mai cin gashin kanta da gundumomin Wenchuan da Li da Heishui da Songpan na lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin. Bisa kididdigar da aka yi a shekara ta 2000, yawan mutanen kabilar ya kai kimanin dubu dari 3. Suna da yaren Qiang, amma babu kalmomi da haruffa.

'Yan kabilar Qiang sun dade suna nan kasar Sin. Yau da shekaru fiye da dubu 3 da suka wuce, kakanin-kakanin 'yan kabilar Qiang suka fara kaura zuwa yankunan da ke lardin Sichuan na yanzu daga lardunan Gansu da Qinghai, kuma sun nemi aure a tsakaninsu da sauran mutanen kabilun kasar Sin. Sannu a hankali ne kabilar Qiang ta yanzu ta bullo a lardin Sichuan.

A da, zaman al'ummar kabilar Qiang tana cikin halin koma baya, 'yan kabilar sun yi aikin gona ne da wukake da wuta kawai. Amma, bayan da aka kafa gundumar Maowen ta kabilar Qiang mai cin gashin kanta a ran 7 ga watan Yuli na shekarar 1958, 'yan kabilar Qiang sun sami ikon mulkin kansu. Tattalin arzikin kauyuka na gundumar ya samu cigaba cikin sauri, yawan hatsin da suka samu ya yi ta samun karuwa a kai a kai a kowace shekara. Sauran sana'o'in da 'yan kabilar Qiang suke yi sun kuma samu cigaba. Sa'an nan kuma, an fara raya masana'antun yin takardu da sarrafa katako da yin siminti da takin zamani a yankunan da 'yan kabilar suke zama. Musamman 'yan kabilar sun kara gina dam domin samar da wutar lantarki. Yanzu gidajen 'yan kabilar da suka kai kashi 97 daga cikin kashi dari na dukkan gidajen 'yan kabilar suna amfani da wutar lantarki. Bugu da kari kuma, a da, babu hanyoyin mota a yankunan kabilar Qiang, amma yanzu an riga an shimfida hanyoyin mota masu dimbin yawa da suke hada kusan dukkan wuraren da 'yan kabilar suke zama tare da gina makarantu da asibitoci da dakunan jiyya. Yanzu, yara wadanda suke karatu a makarantun firamare da na sakandare sun kai kashi 95 daga cikin kashi dari na dukkan yaran kabilar.

Kabilar Qiang tana da fasahohin zane-zane da al'adun musamman. Wakoki da tatsuniyoyin kabilar suna shafar abubuwa iri iri, ciki har da zaman rayuwar yau da kullum da soyayya da shagulgula na kabilar.

'Yan kabilar Qiang suna cin masara da alkama da dankali, kuma sun fi son shan giyar da suka yi da shinkafa da kansu. Gidajen da suka gina da kansu suna da benaye 3, wato a bene na farko, ana kiwon dabbobin gida, iyalai suna kwana a bene na biyu, sa'an nan kuma suna ajiye hatsi a bene na uku. Bisa al'adar kabilar Qiang, kowane saurayi dan kabilar Qiang yana iya auren mace daya, miji yana da iko sosai a cikin gidansa. Matasa ba su da 'yancin zaben abokan aurensu, sai iyayensu ne suke nema musu aure.

'Yan kabilar Qiang suna bin addinin Lama, wata darikar addinin Budda da yake yaduwa a yankunan da ke dab da jihar Tibet.(Sanusi Chen)