Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-30 19:14:23    
Kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa ya kaddamar da babbar kyauta ga mata a fannin wasan motsa jiki a shekarar 2007

cri

A ran 3 ga watan Maris na wannan shekara wato ranar bikin matan duniya, akwai mata guda shida na duniya da suka samu kyauta mai daraja, wato babbar kyauta da kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa ya samar musu saboda fitaccen taimakon da suka bayar a fannin wasannin motsa jiki na duniya da kuma yayata akidar wasannin motsa jiki.

Domin yaba wa wadancan mutane ko kungiyoyi, wadanda suka rinka sa kaimi ga mata da su shiga harkokin wasannin motsa jiki, kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa ya kaddamar da wannan babbar kyauta. Manyan bangarori biyar kowanensu na samun lambar yabo guda, kuma akwai wata babbar lambar yabo ta duniya. Kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin ta taba samun lambar yabo ta Asiya ta shekarar 2000 sakamakon muhimmiyar rawa da ta taka wajen daukaka ci gaban wasan kwallon kafa na mata.

An labarta, cewa mata daga kasar Kenya, da kasar Amurka, da Palasdinu, da kasar Jamus da kuma kasar Papua and New Ghinea, kowanensu ya samu lambar yabo a madadin Afrika, da Latin-Amurka, da Asiya, da Turai da kuma Oceania. Firaministar kasar Jamaica Madam Portia Simpson Miller ta samu babbar lambar yabo ta duniya. Wannan shahararriyar 'yar siyasa ta taba zama ministar wasannin motsa jiki na wannan kasa cikin dogon lokaci. Hakan kasar Jamaica ta samu manyan nasarorin da suka jawo hankulan kasashen duniya.

Jama'a masu saurare, tun da akwai sauran lokaci , bari in dan gutsura muku wani bayani na game da yadda gwamnatin birnin Beijing take kokari matuka wajen kyautata aikin hidima na wasannin motsa jiki musamman domin taron wasannin Olympic.

Aminai, ko kuna sane da, cewa a shekara mai zuwa wato shekarar 2008, za a gudanar da gagarumin taron wasannin Olympic a nan birnin Beijing. Yanzu dai, gwamnatin birnin Beijing tana yin aikin share fage da yin amfan da wannan izni don kara karfafa karfin bada hidima ga taron wasannin motsa jiki; haka kuma za a samar da hidima mai kyau ga mazauna birnin. Saboda haka, kwanakin baya dai, hukumar kula da wasannin motsa jiki ta birnin Beijing ta yi shelar daukar jerin matakai.

A ran 28 ga watan Fabrairu da ya gabata, a cibiyar watsa labarai ta taron wasannin Olympic ta Beijing, hukumar kula da wasannin motsa jiki ta birnin Beijing ta shirya wani taron watsa labarai kan yanayin aikin motsa jiki da dukkan jama'ar birnin ke ciki, inda wani babban jami'in hukiumar din ya bayyana, cewa a shekarar da muke ciki, gwamnatin birnin Beijing za ta ci gaba da samar da gine-ginen wasannin motsa jiki masu inganci ga mazauna birnin, ta yadda za su ji dadin da wasannin motsa jiki ke kawo musu.

Jama'a masu saurare, a shekarar da muke ciki, gwamnatin birnin Beijing za ta shirya wasu ayyukan al'adun wasannin Olympic a jere. Ana kyautata zaton, cewa za a shirya manyan harkokin wasannin motsa jiki da yawansu zai kai goma sha daya, wadanda a ciki suke kunshe da gasar wasan kwallon tebur, da ta wasan kwallon kafa, da ta wasan kwallon kwando da kuma ta wasan kwallon badminton da dai sauransu.

Domin kara karfafa sha'awar mazauna birnin Beijing kan wasannin motsa jiki, gwamnatin birnin Beijing za ta shirya manyan gasannin duniya guda goma, kamar su wasan kwallon rugby da na kwallon kafa da na wasan billiards, da kuma na wasan tennis da dai sauransu. Kazalika, domin kara karfafa ilmin wasannin motsa jiki na mazauna birnin, za a kafa wani dandamali domin gabatar da izni ga mazauna birnin da su yi cudanya da gogaggun 'yan wasa. Dadin dadawa, mun samu labarin, cewa don kara kyautata sharudan wasannin motsa jiki ga mazauna birnin, yanzu ana yin aikin share fage domin gabatar da wani irin kati ga mazauna birnin, wato ke nan muddin mazauna birnin Beijing sun ajiye kudi kadan a cikin katin, to za su iya shiga dukkan club-club a duk fadin birnin Beijing domin yin wasannin motsa jiki kamar yadda suke so. ( Sani Wang )