Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-30 19:13:24    
Masana'antun kasashen waje a kasar Sin suna kokarin bin manufofin dacewa da halin kasar

cri

Tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude wa kasashen waje kofa a karshen shekarun 1970, masana'antun kasashen waje wadanda ke zubawa jari a kasar sun yi ta karuwa. Masana'antun suna mai da hankali sosai wajen bin manufofin da suka dace da halin da ake ciki a kasar dangane da al'adu da kasuwanci, ta yadda za su saba wa kasuwannin kasar Sin tun da wuri. Bisa kokarin da suka yi ta yi a cikin shekaru da yawa da suka wuce, yanzu, masana'antun sun fara samun sakamako mai kyau, kuma suna ta kara zurfafa irin wadannan manufofinsu.

Bisa al'adun gargajiya na kasar Sin, mutane su kan yi wa juna barka da sabuwar shekara a lokacin bikin bazara wato ranar sabuwar shekara bisa kalandar garagajiya ta manoman kasar Sin. A gabannin bikin bazara na wannan shekara, masana'antun kasashen waje sama da 10 da ke a kasar Sin kamar kamfanin Siemens da kamfanin sadarwa na Korea ta Kudu da sauransu sun hada kansu sun yi wa jama'ar Sin barka da sabuwar shekara ta hanyar tallace-tallace da sauran hanyoyin watsa labaru.

A gun taron manema labaru da aka shirya a gabannin bikin bazarar, a madadin kamfanonin kasashen waje a kasar Sin, malama Wang Xin, manajar reshen kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na kasar Korea ta Kudu da ke a kasar Sin ta yi wa duk jama'ar kasar Sin barka da sabuwar shekara kafin bakin bazara ya zo. Ta ce, "a lokacin kusantowar ranar bikin bazara, ina yi wa duk jama'ar kasar Sin barka da sabuwar shekara, ina fatan jama'ar da dama za su kara daukar jiragen sama na kamfaninta wajen yin tafiya, kuma za su kara jin dadin tafiyarsu kwarai."

Bisa kididdigar da ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta yi, an ce, ya zuwa karshen watan Satumba na shekarar bara, yawan masana'antu da aka amince da kafa su a kasar Sin bisa jarin kasashen waje ya kai dubu 580, yawan kudin jarin nan da aka kashe ya kai dalar Amurka biliyan 665. Masana'antun kasashen waje da yawa sun fara samun sakamako mai kyau ta hanyar aiwatar da manufofin da suka dace da kasar Sin. Manufofin sun shafi fannonin daukar ma'aikatan kasar Sin da kwararrunta da huldar jama'a da kayayyyaki da kasuwanni da sauransu.

Madam Song Ling, shugabar kungiyar kasuwancin electron ta kasar Sin ta nuna babban yabo ga harkokin da masana'antun kasashen waje suka shirya cikin hadin guiwarsu don yi wa jama'ar Sin barka da sabuwar shekara. Ta ce, "msana'antun kasashen waje a kasar Sin sun iya yi wa jama'ar kasar Sin barka da sabuwar shekara bisa burinsu, wannan ya nuna cewa, lalle, suna kokari don sabawa da halin da ake ciki a kasar dangane da tattalin arziki da al'adu, harkokin nan kuma sun sami karbuwa daga wajen jama'ar Sin a fannoni daban daban. "

Masana'antun kasashen waje a kasar Sin suna dora muhimmanci sosai wajen fitar da kayayyaki da masaya na kasar ke bukata. Alal misali, tun bayan da wani kamfanin kasar Amurka da ake kira Procter & Gamble a Turance ya shiga kasuwannin kasar Sin a shekarun 1980, bai taba ambatar sunan Amurka a cikin duk tallace-tallace da ya yi a kasar Sin ba, kuma ya sami duk sunayen kayayyakinsu ne, bayan da aka yi bincike-bincike sosai a kasar, don haka ya sami karbuwa sosai daga wajen masaya na kasar Sin.

Malam Cao Hengwu, shugaban kungiyar jaridun masana'antu ta kasar Sin ya nuna cewa, "a cikin shekarun nan da suka wuce, masana'antun kasashen waje da yawa sun sami sakamako mai kyau a kasar Sin, kuma sun sami karbuwa sosai daga wajen jama'ar kasar. A ganina, wani babban dalilin da ya sa haka shi ne domin suna bin manufofin da suka dace da halin da kasar Sin ke ciki. Sabo da haka wajibi ne, masana'antu da ke neman samun kyakkaywan sakamako da wadanda za su zuba jari a kasar nan gaba kadan su bi wadannan manufofi. " (Halilu)