Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-29 19:01:32    
Saukakakken tarihi na shugabannin kasar Sin.(Babi Daya)

cri

Da farko ina so in gabatar da Mr Hu Jintao,shi ne sakatare-janar na kwamitin tsakiya na Jam"iyyar Kwaminis ta Sin,kuma shugaban kwamitin soja na tsakiya na jamhuriyar jama'ar kasar Sin.Shi mutumin na kabilar Han ne.An haife shi a wurin Jixi na lardin Anhui na kasar Sin a watan Disamba na shekara ta 1942.

Daga shekara ta 1959 zuwa shekara ta 1964,ya yi karatu a sashen koyon ilim dangane da ayyukan ban ruwa a jami'ar Qinghua,haka kuma ya yi karatu a fannin nan har zuwa shekara ta 1965,a wannan shekara yana kan matsayin mai ba taimako a fannin siyasa (wato political instractor).Daga shekara ta 1965 zuwa shekara ta 1968,ya yi nazari da binciken aikin kimiyya da kasancewa mai da taimako a fannin siyasa.(har zuwa somawar "juyin juya hali na al'adu".Daga shekara ta 1968 zuwa shekara ta 1969,ya zama ma'aikaci na kungiyar gina gidaje na hukumar kula da madatsar ruwa ta Liu Jiaxia ta ma'aikatar ban ruwa ta kasar Sin.Daga shekara ta 1969 zuwa shekara ta 1974,ya taba zama mallamin fasaha da sakatare da kuma mataimakin sakatare na reshen jam'iyyar na sashe 813 na hukumar kula da ayyuka ta hudu ta ma'aikatar ban ruwa ta kasar Sin.Daga shekara ta 1974 zuwa shekara ta 1975,ya zama sakatare na kwamitin gine gine na gwamnatin lardin Gansu.Daga shekara ta 1975 zuwa shekara ta 1980,ya zama mataimakin darektan ofishin kula da tsara fasali na kwamitin gine-gine na gwamnatin lardin Gansu.Daga shekara ta 1980 zuwa shekara ta 1982,ya kasance mataimakin shugaban kwamitin gine gine na lardin Gansu kuma sakatare na kwamitin lardin Gansu na kungiyar samari 'yan kwaminis ta kasar Sin(daga satumba zuwa Disamba na shekara ta 1982).Daga shekara ta 1982 zuwa shekara ta 1984,ya kasance sakatare na sashen sakatariya na kwamitin tsakiya na kungiyar samari 'yan kwaminis ta Sin haka kuma shugaban kawancen samari na duk kasa baki daya.Daga shekara ta 1984 zuwa shekara ta 1985,yana kan matsayin sakatare na farko na sashen sakatariya na kwamitin tsakiya na kungiyar samari 'yan kwaminis ta Sin.Daga shekara ta 1985 zuwa shekara ta 1988,yana kan matsayin sakatare na kwamitin lardin Guizhou kuma sakatare na farko na kwamitin jam'iyyar na rukunin soja na lardin Guizhou.Daga shekara ta 1988 zuwa shekara ta 1992,yana kan matsayin sakatare na kwamitin jam'iyyar na jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta kuma sakatare na farko na kwamitin jam'iyyar na rukunin soja na Tibet.Daga shekara ta 1992 zuwa shekara ta 1993 yana kan matsayin zaunannen mamban ofishin siyasa na tsakiya kuma sakatare na sashen sakatariya na tsakiya.Daga sshekara ta 1993 zuwa shekara ta 1998,yana kan matsayin zaunannen mamban ofishin siyasa na tsakiya da sakatare na sashen sakatariya na tsakiya da kuma shugaban makarantar nazarin ilimin jam'iyya na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin.Daga shekara ta 1998 zuwa shekara ta 1999,yana kan matsayin zaunannen manban ofishin siyasa na tsakiya kuma sakatare na sashen sakatariya na tsakiya da mataimakin shugaban kasa na jamhuriyar jama'ar Sin da shugaban makarantar koyon ilimin jam'iyya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin. Daga shekara ta 1999 zuwa shekara ta 2002,yaana kan matsayin zaunannen manban ofishin siyasa na tsakiya,kuma sakataren sashen sakatariya na tsakiya,kuma mataimakin shugaban kwamitin soja na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin,kuma mataimakin shugaban Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin da mataimakin shugaban kwamitin soja na tsakiya na jamhuriyar jama'ar kasar Sin da shugaban makarantar koyon ilimin jam'iyya na tsakiya.Daga shekara ta 2002 zuwa watan Maris na shekara ta 2003,yana kan matsayin sakatare-janar na kwamitin tsakiya kuma mataimakin shugaba na kwamitin soja na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin,kuma mataimakin shugaban jamhuriyar jama'ar kasar Sin kuma mataimakin shugaban kwamitin soja na tsakiya na jamhuriyar jama'ar kasar Sin da shugaban makarantar koyon ilimin jam'iyya na tsakiya.(daga watan Disamba na shekara ta 2002 ya bar gurbin nan na shugaban makarantar).

Daga watan Maris na shekara ta 2003 zuwa watan Satumba na shekara ta 2004,yana kan matsayin sakatare-janar na kwamitin tsakiya kuma mataimakin shugaban kwamitin soja na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin,shugaban Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin da mataimakin shugaban kwamitin soja na tsakiya na Jamhuriyar Jama'ar Kasar Sin.Daga watan Satumba na shekara ta 2004 zuwa watan maris na shekara ta 2005,yana kan matsayin sakatare-janar na kwamitin tsakiya kuma shugaban kwamitin soja na tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da kuma shugaban Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin da mataimakin shugaban kwamitin soja na tsakiya na Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin.

Daga watan Maris na shekara ta 2005 har zuwa yanzu yana kan matsayin sakatare-janar na kwamitin tsakiya kuma shugaban kwamitin soja na tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin,da kuma shugaban Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin da shugaban kwamitin soja na tsakiya na Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin.

Mr Hu Jintao yana kan matsayin mamban ba cikakke ba kuma manban kwamitin tsakiya na 12 na JKS,da mamban kwamitin tsakiya na 13,14,15,da 16,yana kan matsayin mamba da zaunannen manba na ofishin siyasa da sakataren sashen sakatariya na kwamitin tsakiya na 14 da 15 na jam'iyyar kwaminis ta Sin,kuma manban da zaunannen manba na ofishin siyasa na kwamtin tsakiya na 16 na JKS.ya taba kasance mamban na kwamitin dindindin na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin.

Matarsa Liu Yongqing,suna da da daya da 'ya daya.