Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-29 18:26:40    
Kasar Sin ta bayar da tsarin raya harkokin kananan kabilun kasar

cri

A kwanan baya, kasar Sin ta bayar da tsarin raya harkokin kananan kabilunta tsakanin shekara ta 2006 da ta 2010. A ran 29 ga wata, a nan birnin Beijing, Tondrup Wangden, mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin kabilun kasar Sin ya ce, wannan tsari yana da muhimmiyar ma'ana kan yadda za a raya tattalin arziki da zaman al'umma na kananan kabilun kasar cikin halin daidaito, ta yadda za a iya tabbatar da iko da moriya na halal na kananan kabilu da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ksasar Sin.

Kasar Sin kasa ce da ke da kabilu iri iri. Ban da kabilar Han wadda take da mutane masu yawan gaske, tana da kananan kabilu 55 da yawan mutanensu ya kai dubu dari 1 ko fiye, wato ya kai kashi 8 cikin kashi dari bisa na duk yawan mutanen kasar. Mr. Tondrup Wangden, mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin kabilun kasar Sin, ya ce, a kullum gwamnatin kasar Sin tana goyon bayan raya harkoki iri iri na kananan kabilun kasar. Bayan da aka fara tafiyar da manufofin yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin, musamman bayan da aka fara tafiyar da shirin raya yankuna na yammacin kasar, harkokin da suke shafar kananan kabilun kasar sun samu ci gaba kwarai. Amma har yanzu, yankunan kananan kabilun kasar suna koma baya. Ya ce, "A sakamakon matsaloli iri iri da suka kasance a cikin tarihi da zaman al'umma da na halittu, har zuwa yanzu, yankunan kananan kabilun kasar Sin suna koma baya. Tattalin arziki da zaman al'umma suna samun cigaba cikin halin rashin daidaito a tsakanin kanannan kabilu daban daban da yankuna daban daban. A waje daya kuma, ana samun bamban sosai a tsakanin yankuna daban daban da a tsakanin garuruwa da kauyuka tare da kuma a tsakanin kabilu daban daban. Irin wannan halin da ake ciki yana kawo illa ga yunkurin raya wata zaman al'umma mai jituwa a kasar Sin."

Wannan jami'i, wani dan kabilar Tibet, ya ce, makasudin tsara wannan tsari shi ne daidaita matsalolin da suke jawo hankula mutane sosai kuma suke kasancewa a gaban kananan kabilun kasar. A cikin tsarin, an jaddada cewa za a kara mai da hankali kan daidaita batutuwan ilmi da kiwon lafiya da ba da tabbaci ga jama'a da sauran batutuwan da suke shafar ingancin zaman rayuwar jama'a.

Alal misali, game da batun ilimi, za a sauke nauyin aiwatar da manufar ba da ilmin tilas na tsawon shekaru 9 a shekara ta 2010 a yankunan kananan kabilun kasar Sin. A waje daya, za a yi kokarin kyautata sharudan jami'o'in kananan kabilun kasar yayin da ake kiyaye sabbin ilmi game da magunguna da muhalli da kiwon lafiyarsu tare da kuma daidaita matsalolin da daliban kananan kabilu masu fama da talauci suke fuskanta.

Game da batun kiwon lafiyar 'yan kananan kabilun kasar, an bayyana cewa, nan da shekaru masu zuwa, gwamnatin kasar Sin za ta kara mai da hankali kan yadda za a kafa sabon tsarin likitanci na hadin kai da horar da likitoci da fama da cututtuka masu tsanani a yankunan kananan kabilu. Bugu da kari kuma, za a kara yin watsi da kuma yin rigakafin annobar ciwace-ciwace a yankunansu da ciwace-ciwacen da suke faruwa a yankunansu kawai. Haka kuma, za a kara karfin kiyaye magungunan gargajiya na kananan kabilu da kuma yada ilmin kiwon lafiya da yin rigakafin ciwace-ciwace iri iri ga jama'ar kananan kabilun kasar.

Haka kuma, game da batun ba da tabbaci ga jama'ar kananan kabilu, a cikin wannan tsarin da aka bayar a kwanan baya, an ce, za a kyautata matsayin jin dadin al'ummomin kananan kabilun kasar a kai a kai, da kafa tsarin ba da tabbaci ga jama'a, ta yadda wannan tsari zai ba da taimako ga jama'a masu yawa.

Bugu da kari kuma, a cikin wannan tsari, lokacin da ake jaddada raya kananan kabilu, ana kuma jaddada kiyaye al'adun kananan kabilun kasar. Mr. Tongdrup Wangden ya ce, "Muna kiyaye da raya al'adun kananan kabilu ne bisa ka'idojin dokokin kasar. A cikin 'Dokar tafiyar da harkokin kananan kabilun kasar da kansu', an bayyana cewa, dukkan larduna da jihohi da manyan birane da gundumomi da shiyyoyi suna da dokar kiyaye al'dun kananan kabilun kasar. Ina cike da imani cewa, bayan aiwatar da wannan sabon tsarin raya harkokin kananan kabilun kasar Sin a tsakanin shekara ta 2006 da ta 2010, aikin kiyaye da kuma raya al'adun kananan kabilun kasar zai kai wani sabon mataki." (Sanusi Chen)