A ran 29 ga wata da safe, shugaban kasar Sin ya komo birnin Beijing ta jirginsa na musamman, bayan da ya kawo karshen ziyararsa a Rasha cikin nasara da kuma halartar bikin bude shagalgulan 'shekarar Sin a Rasha' da na 'nune nunen kayayyakin Sin a Rasha'.
A loakcin ziyararsa a Rasha, shugaba Hu ya gana da Putin da sauran shugabannin kasar Rasha bi da bi, inda bangarorin biyu suka yi musanyar ra'ayoyinsu a kan bunkasuwar dangantakar hadin kai da abokantaka bisa manyan tsare tsare a tsakaninsu da kuma lamuran duniya da shiyya shiyya da suke jawo hankulansu, kuma kasashen biyu sun bayar da sanarwar hadin gwiwa. Shugabannin kasashen biyu kuma sun halarci bikin bude shagalgulan 'shekarar Sin a Rasha' da na 'nune nunen kayayyakin Sin a Rasha'.
A gun ziyarar Hu Jintao a Rasha, manyan kafofin watsa labaru na Rasha sun bayar da labaran ziyarar Hu a kasar. Jaridar 'New Izvestia' ta ce, jama'ar kasar Rasha suna sha'awar 'nune nunen kayayyakin Sin a Rasha' sosai da sosai. Jaridar 'Trud' ta yi amfani da maganar shugaban kasar Rasha Mr Putin cewa, 'fahimtar bunkasuwar tattalin arizkin Sin za ta ba da taimako ga jama'ar Rasha'.
Ban da wannan kuma, kafofin watsa labaru na kasashen Korea ta kudu da Malasiya da Nepel da dai sauransu su ma sun mai da hankali sosai a kan ziyarar Hu Jintao a Rasha.(Danladi)
|