Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-28 21:45:19    
Wani matakin yanayin sararin samaniya na kasar Sin, wato ranar bikin somawar yanayin bazara

cri

Da farko, za mu yi bayani kan ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya na kasar Sin. Game da ranar bikin yanayin sararin samaniya, an bayyana cewa, bisa sauyawar yanayin sararin samaniya da yawan ruwan sama da aka samu da tsawon lokacin saukar jaura da dai sauran almomin halittu ne, aka raba shekara guda don ta zama matakan lokutan bayyana almomin yanayin sararin samaniya karo karo, ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya su ne ranakun somawar wadannan matakan lokutan bayyana almomin yanayin sararin samaniya. Tsara tsarin ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya shi ne sakamakon da jama'ar zamanin aru aru na kasar Sin suka samu a lokacin da suka dudduba da yi nazari kan ilmin yanayin sararin samaniya . Wannan yana da tasiri mai muhimmanci sosai ga harkokin noma. Bisa bayanan da aka tanada, an rubuta cewa, a shekarar 104 kafin bayyanuwar Annabi Isa (A.S), mutanen kasar Sin sun riga sun tsara tsarin ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya, don tunawa da su sosai, mutanen zamanin da sun kuma tsara wakoki dangane da ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya.

 

Yau, za mu yi bayani kan ranar farko da ke cikin wadannan ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya, wato "Leichun"cikin Sinanci. A cikin harshen Sinanci, kalmar "Lei" na da ma'anar somawar abubuwa, ma'anar "Leichun" ita ce ranar somawar yanayin bazara, kuma dukkan abubuwan hallitu suna farkawa a yanayin. Ranar somawar yanayin bazara wato "Leichun" ta yi banbam sosai da bikin gargajiyar kasar Sin na yanayin bazara, lokacin somawar ranar yanayin bazara wato "Leichun" bai yi daidai da lokacin bikin gargajiyar kasar Sin na yanayin bazara ba, in lokacin ranar bikin yanayin bazara ya zo, ba a bayyana cewa, lokacin bikin gargajiyar kasar Sin na yanayin bazara ya zo. Wato ranar somawar yanayin bazara na shekarar da muke ciki ita ce ranar 4 ga watan Fabrairu, wato bayan ranaku 14 ne bikin yanayin bazara na gargajiyar kasar Sin ya zo. Dayake kalandar gargajiyar kasar Sin ta manoma ta yi banban da ta Turawa, shi ya sa ranar somawar yanayin bazara wato ranar "Leichun" ta yi banban sosai da na kowace ranar bikin bisa kalandar Turawa a kowace shekara. Manoma sun fi son ranar somawar yanayin bazara, duk saboda tsire-tsiren halittu sun sake tsiro, kuma naman daji da suke yin barci a yanayin hunturu sun soma farkawa, ranar "Leichun" rana ce da ke juyawar zafin rana da hasken rana da saukar ruwan sama da dai sauransu, bisa albarkacin kara zafin yanayin sararin samaniya, tsire-tsire suna kara kara da sauri, kuma suke kara shan ruwa da yawa , ya kamata a kara musu taki da ruwa. Kasar Sin kasa ce ta mai da hankali sosai ga aikin noma, saboda haka manoma sun mai da hakulansu sosai ga ranar somawar yanayin bazara.

Game da ranar somawar yanayin bazara, a kasar Sin ta zamanin da, an yi shagulgulan murnar ranar da yawa. Bikin maraba da yanayin bazara ya fi muhimmanci, an yi bikin kafin ranar somawar yanayin bazara, makasudin shagalin shi ne don maraba da yanayin bazara da aljannu na yanayin bazara. Kafin bikin, an gina wata rumfa a gonaki da kuma shirya turare da kander da dai sauransu tare da wani yaron da ya kwaikwayi sifar aljanna , kuma an yi amfani da gora da sauran abubuwa don yin wani abun da ke da sifar shanu, an kira shanun din da sunan shanun yanayin bazara, wato "Chunmiu" ke nan cikin sinanci, a cikin cikin "Chunniu", an sanya gyada da sauran busassun 'ya'yan itatuwa da tsabar kudi da sauran abubuwa. Bayan budewar bikin shagalin, sai jami'an kananan hukumomi da jama'ar farar hula sun tashi daga biranen da suke zama zuwa gonaki don karbar aljannar yanayin bazara da shanun yanayin bazara zuwa birane, sa'anan kuma an yi bikin girmamawar shannun da aljannar da barasa , daga nan sai an kawo karshen bikin maraba da yanayin bazara.

A ranar bikin somawar yanayin bazara, mutane su kan cin abincin musamman, yawancin abincin da aka ci su ne irin wani waina na kasar Sin da ke hada da albasa da citta da yaji da dai saruansu, ana cewa, cin irin abinci zai iya shawo kan ciwace-ciwacen da aka kamu da su. (Halima)