Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-28 21:39:46    
Harkar binciken sararin samaniya a kasar Sin

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malam Ibrahim Zubairu Othman, mazaunin zaria, jihar Kaduna, tarayyar Nijeriya. Malam Ibrahim Zubairu Othman ya aiko mana wata wasika, inda ya tambaye mu, shin 'yan saman jannati na kasar Sin suna bayar da gudummowa ga duniya a wajen binciko abubuwan ban mamaki a sararin sama kamar yadda 'yan saman jannati ko masana kimiyya na Amurka da Ingila da Jamus suke yi?

Jama'a masu sauraro, 'yan saman jannati na kasar Sin suna bayar da nasu gudummowa ga duniya a wajen binciken sararin sama. Hakika, Sin ta fara gudanar da harkokin binciken sararin sama ne a shekarun 1950 zuwa 1960. A shekara ta 1958, Sin ta fara gina filinta na farko na harba rokoki masu dauke da taurarin dan Adam. A watan Yuli na shekara ta 1964, Sin ta cimma nasarar harba wata roka mai dauke da halittu, wato wani bera a ciki, wanda ke alamar cigaba na farko da Sin ta samu a wajen binciken sararin sama. Daga baya, a shekara ta 1970, Sin ta kafa hukumar binciken lafiyar 'yan sama jannati, kuma ta fara zabar 'yan sama jannati da kuma horar da su, haka kuma Sin ta fara gudanar da harkokin binciken lafiyar 'yan sama jannati. Sa'an nan, a watan Afril na shekara ta 1970 a birnin Jiuquan na kasar Sin, a karo na farko ne Sin ta cimma nasarar harba wani tauraron dan Adam wanda ke da suna "Dongfanghong No.1", sakamakon hakan kuma, Sin ta zama kasa ta biyar a duniya wadda ke iya harba taurarin dan Adam. Sa'an nan a shekarar 1975, Sin ta cimma nasarar harba wani tauraron dan Adam da ake iya komo da shi, kuma bayan kwanaki uku, ta komo da shi nan doron duniya lami lafiya. Sabo da haka kuma, kasar Sin ta zama kasa ta uku a duniya wadda ke mallakar fasahar komo da tauraron dan Adam.

A shekara ta 1985, a hukunce ne Sin ta yi shelar shigar da jerin rokokinta na Changzheng cikin kasuwar harba rokoki ta duniya. A shekarar 1990 kuma, wata roka mai suna Changzheng No.3 ta kasar Sin ta harba wani tauraron dan Adam da Amurka ta kera cikin nasara. A shekara ta 1990 kuma, Sin ta cimma nasarar harba wata roka mai suna Changzhen No.2, kuma rokar na iya daukar nauyi har ton 9.2, wanda har ya share fage a wajen harba kumbo mai dauke da dan Adam.

A ran 15 ga watan Oktoba na shekarar 2003, Sin ta harba wani kumbo mai dauke da dan Adam wanda ke da sunan Shenzhou No.5 cikin nasara, kumbon dai yana daukar wani dan saman jannati na kasar Sin, wato malam Yang Liwei, wanda ke daya daga cikin 'yan saman jannati na farko da kasar Sin ta horar. Bayan da kumbon ya shafe awa 21 da minti 23 yana zagaye duniya har sau 14, ya dawo doron kasa lami lafiya.

Daga baya a watan Oktoba na shekara ta 2005, Sin ta cimma nasarar harba wani kumbo daban mai dauke da mutane, haka kuma wannan karo na farko ne da Sin ta aika da 'yan sama jannati biyu cikin sararin samaniya a lokaci guda.

Masu saurare, mun dai yi muku dan bayani kan tarihin binciken sararin samaniya na kasar Sin, don amsa tambayar da malam Ibrahim Zubairu Othman, mazaunin zaria, jihar Kaduna, tarayyar Nijeriya ya yi mana. Hakika, Sin tana kuma aiwatar da hadin gwiwa da Nijeriya a bangaren harkokin sararin samaniya.

A ran 15 ga watan Disamba na shekarar 2004, Sin ta rattaba hannunta kan wata kwangila tare da hukumar binciken sararin samaniya ta Nijeriya. Bisa kwangilar, Sin za ta samar wa Nijeriya wani tauraron dan Adam irin na sadarwa, don biyan bukatun Nijeriya a fannin sadarwa da watsa labarai da dai sauransu. An ce, Sin za ta harba tauraron cikin roka irin na Changzheng No.3, kuma za ta gina tashoshi biyu a doron kasa, wato daya a Abuja, babban birnin Nijeriya, dayan kuma a birnin Kash da ke jihar Xinjiang ta kasar Sin, za ta kuma samar da hidima a wajen sarrafa shi da horar da ma'aikata.(Lubabatu)