Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-28 14:22:17    
Shugabannin kasashen Sin da Rasha sun halarci bikin bude shagalin 'nune nunen kayayyakin Sin'

cri

A ran 27 ga wata, shugaban kasar Sin Hu Jintao wanda yake ziyara a kasar Rasha da takwaransa na Rasha Vladimir Putin sun halarci bikin bude shagalin 'nune nunen kayayyakin Sin'. A ran nan kuma, shugaba Hu ya gana da firayin ministan Rasha Mikhail Fradkov da shugaban majalisar Duma Doris Gryzlov bi da bi.

Babban take na shagalin 'nune nunen kayayyakin Sin' shi ne, hadin kai da moriyar juna da kuma samun bunkasuwa mai jituwa. Shagalin nune-nunen kayayyakin Sin a Rasha ya fi girma bisa matakin nune-nunen da aka yi a kasashen waje ta fuskar fannoni da yawa.

A gun bikin budewar, shugaba Hu ya bayar da wani jawabi cewa, ta aikace aikacen da aka shirya a gun shagalin 'nune nunen kayayyakin Sin', kasar Sin tana fatan cewa, za ta bayyana dadadden tarihin kasar Sin da kuma kyawawan al'adunta, da kuma yunkurin yin gyare gyare a gida da bude kofa ga duniya da sha'anin maida kasar Sin ta zamani da ake gudanarwa, da kuma nasarorin da aka samu daga hadin kan Sin da Rasha a fannonin tattalin arziki da cinikayya ga jama'ar kasar Rasha.

Mr Puti ma ya bayyana cewa, har kullum kasar Sin tana zama wata muhimmiyar kawar Rasha a fannonin tattalin arziki da cinikayya. Shagalin 'nune nunen kayayyakin Sin' da aka shirya ba zai kara yawan cinikayyar da bangarorin biyu suke yi kawai ba, har ma zai iya kara ingancinsu.

A gun ganawar shugaba Hu da firayin ministan Rasha Mikhail Fradkov, Hu Jintao ya jaddada cewa, kamata ya yi kasashen Sin da Rasha su kara amincewa da juna a fannoni daban daban, su kara zurfafa hadin kansu, su kara taimakawa juna a kan harkokin duniya da na shiyya shiyya, ta yadda za a iya sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar hadin kai da abokantaka a tsakaninsu.

A yayin da yake yin shawarwari da shugaban majalisar Duma Doris Gryzlov, Hu Jintao ya fadi cewa, kara raya dangantakar hadin kai da abokantaka a tsakanin Sin da Rasha tana da ma'ana mai zurfi a yanzu kuma a tarihi. Kasar Sin tana son yin kokari tare da Rasha domin kara inganta dangantakarsu.(Danladi)