Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-28 08:46:54    
`Yan wasan salon iyo na kasar Sin suna yin kokari bisa taimakon malamar wasarsu daga kasar Japan domin taron wasannin Olimpic na Beijing

cri

Masu sauraro,a halin da ake ciki yanzu,ana yin zama na 12 na gasar cin kofin duniya na wasan iyo a birnin Melburne na kasar Australia.A gun gasar wasan salon iyo tsakanin mata biyu biyu da aka yi a ran 20 ga wata,`yan wasa daga kasar Sin Jiang Wenwen da Jiang Tingting sun samu lamba ta hudu,wannan sakamako mafi kyau ne da `yan wasan salon iyon kasar Sin suka samu a cikin manya gasannin duniya.Dalilin da ya sa haka shi ne domin `yan wasan salon iyo na kasar Sin suna sanya matukar kokari a karkashin taimakon malama Masayo Imura,babbar malamar koyar da wasan salon iyo wadda ta zo daga kasar Japan.A kasar Japan,ana kiran malama Masayo Imura da sunan `uwar wasan salon iyo`,wato ta yi suna sosai a kasar.A birnin Melburne,malama Masayo Imura ta bayyana cewa,tana fatan kungiyar wasan salon iyo ta kasar Sin za ta samun sabon ci gaba a gun taron wasannin Olimpic da za a yi a birnin Beijing a shekarar 2008.A cikin shirinmu na yau,bari mu yi muku bayani kan wannan.

A gun zagaye na karshe na gasar da aka yi a ran 20 ga wata,`yan wasa daga kasar Sin Jiang Wenwen da Jiang Tingting sun yi nune-nune a cikin ruwa tare da kida mai dadin ji,`yan kallo su ma suna jin dadi sosai,amma a da `yan wasan salon iyo na kasar Sin ba su taba samun lambobin yabo a cikin manyan gasannin duniya ba,shi ya sa alkalan wasa ba su saba da wannan ba,sun samun lamba ta hudu kawai.Duk da haka,sun riga sun samun babban ci gaba.Game da wannan,malama Masayo Imura ta ce:  `Ban gamsar da sakamakon da suka samu ba,kodayake ba dole ba ne su samun lambar yabo,amma kamata ya yi su kyautata nune-nunensu saboda suna da wannan iyawa.`

Jiang Wenwen da Jiang Tingting su tagwaye ne,sun taba zama zakatu a gun taron wasannin Asiya na Doha a shekarar bara,malama Masayo Imura tana ganin cewa,wadannan `yan wasa biyu suna da sharuda masu kyau,suna da daguwar kafa,kuma suna iya gane tunanin juna cikin sauri saboda su tagwaye ne.Amma `yan wasan salon iyo na kasar Sin ba su da babban karfi kamar yadda `yan wasan kasashen Turai suke ba.Yanzu dai,duk wadannan matsaloli suna samun kyautatuwa a kai a kai a karkashin taimakon malama Masayo Imura.

Malama Masayo Imura ta taba zama wata `yar wasan salon iyo a kasar Japan,bayan ta yi ritaya,sai ta fara koyar da wasan salon iyo a kungiyar kasar Japan.Daga shekarar 1984,a karkashin kokarinta,kungiyar wasan salon iyo ta kasar Japan ta taba samun lambobin yabo 8 a gun taron wasannin Olimpic.Domin wannan kuwa,ana kiranta da sunan `uwar wasan salon iyo ta kasar Japan`.

A farkon wannan shekara wato lokacin da malama Masayo Imura ta sanar da cewa,za ta zo kasar Sin koyar da wasan salon iyo a kasar Sin,mutane da yawa a kasar Japan ba su fahimtar da tunaninta ba,har wasu kafofin watsa labarai sun zarge ta da babbar murya.`Dan jarida wanda ke aiki a jaridar `Wasannin motsa jiki na kasar Japan` Shuto Masashi shi ma bai fahimta ba,ya ce: `Wasan Judo da wasan salon iyo na kasar Japan sun fi yin suna a Asiya da duniya,me ya sa `yar kasar Japan ta je kasar Sin koyar da wasan salon iyo?Saboda `yan wasan kasashen nan biyu za su yi takara da juna a gun taron wasanni,shi ya sa ba mu ji dadi ba,amma kan wasanni ne kawai,ba ruwan siyasa.`

Game da wannan,malama Masayo Imura ta karfafa cewa,makasudin zuwanta a kasar Sin shi ne don kara karfafa zumuncin dake tsakanin kasar Sin da kasar Japan,tana fatan cudanya tsakanin kasar Sin da kasar Japan wajen wasan salon iyo za ta kara karfafuwa.Yanzu dai tana jin farin ciki kwarai da gaske saboda ta riga ta samun fahimci daga wajen `yan uwanta.A kwana a tashi,wasu mutanen kasar Japan sun riga sun zama masu goyon bayan kungiyar wasan salon iyo ta kasar Sin.Malama Masayo Imura ta ce,  `A farkon wannan shekara,yayin da mutanen kasar Japan suka ji kudurina,wato zan zo kasar Sin koyar da wasa,wasu sun yi fushi,amma yanzu sun yi hakuri,wasu daga cikinsu sun aiko mini Email inda suka bayyana cewa suna fatan zan daga matsayin wasan salon iyo na kungiyar kasar Sin.Ni ma ina fatan kungiyar kasar Sin za ta samun ci gaba a bayyane a gun taron wasannin Olimpic na Beijing ta yadda kasashen duniya za su gane kungiyar kasar Sin kungiya ce mai karfi.`

To,jama`a masu sauraro,karshen shirinmu na yau ke nan,ni Jamila da na gabatar nake cewa,ku zama lafiya,sai makon gobe war haka idan Allah ya kai mu.(Jamila Zhou)