Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-28 08:45:30    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (21/03-27/03)

cri

Kwanakin baya,kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na birnin Beijing ya nada mutane 21 da su zama manajojin cibiyoyin wasannin motsa jiki na taron wasannin Olimpic na nakasassu na Beijing,wadannan manajoji za su dauki nauyin aikin share fage na taron wasannin Olimpic na nakasassu na Beijing bisa wuyansu.A karshen wannan wata,za a horar da su,daga baya kuma za su fara aiki,a watan Mayu mai zuwa,za su shiga ajin musamman da kwararrun mutane na kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na nakasassu na duniya za su shirya musu,haka kuma za su tafiyar da aiki kamar yadda ya kamata.

Ran 26 ga wata,aka kawo karshen dukkan gasannin tsinduma cikin ruwa na zama na 12 na gasar cin kofin duniya na wasan iyo a kasar Australia,a cikin dukkan lambobin zinariya 10,kungiyar `yan wasan kasar Sin ta samu tara daga cikinsu,wannan shi ne sakamako mafi kyau da kungiyar `yan wasan tsinduma cikin ruwa na kasar Sin ta samu a gun gasar cin kofin duniya a tarihinta.

Ran 24 ga wata,a birnin Melburne na kasar Australia,hadaddiyar kungiyar wasan iyo ta duniya ta sanar da cewa,birnin shanghai na kasar Sin ya samu iznin shirya zama na 14 na gasar cin kofin duniya na shekarar 2011,wannan shi ne karo na farko da kasar Sin ta samu iznin shirya irin wannan gasa.

Ran 21 ga wata,a gun gasar cin kofin duniya na wasan kankara salo-salo da aka yi a birnin Tokyo na kasar Japan,`yan wasa daga kasar Sin Shen Xue da Zhao Hongbo sun zama zakaru,`yan wasa daga kasar Sin Pang Qing da Tong Jian sun zama lambatu wato sun samu lambar azurfa.(Jamila Zhou)