A ran 27 ga wata, shugaban kasar Sin Hu Jintao wanda ke yin ziyara a kasar Rasha da takwaransa na kasar Vladimir Putin sun halarci bikin bude shagalin nune-nune na kasar Sin.
An mayar da "hadin gwiwa don samun moriya tare, da samun bunkasuwa cikin jituwa" a matsayin babban take na wannan shagalin da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta shirya. Kuma shagalin shi ne bikin nune-nune mafi girma da gwamnatin kasar Sin ta shirya a kasashen waje.
A gun bikin, shugaba Hu ya ba da jawabin cewa, ta shagalin, za a nuna wa jama'ar Rasha dogon tarihi da al'adun gargajiya na kasar Sin, da yunkurin bude kofa ga kasashen waje da kuma yin gyare-gyare a gida da Sin ke yi, da kuma sakamako mai kyau da Sin da Rasha suka samu wajen hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya.
Ban da wannan kuma shugaba Putin ya bayyana cewa, shagalin zai zama wata muhimmiyar taga ga kasar Rasha wajen fahimtar manufar bude kofa ga kasashen waje ta kasar Sin. Ya ce, ya yi imanin cewa, ba kawai shagalin zai ba da taimako wajen kara karuwar yawan cinikayya tsakanin kasashen biyu ba, har ma zai taimaka wa bangarorin biyu wajen kyautata ingancin kayayyaki.(Kande Gao)
|