Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-27 18:48:36    
Yawan binciken lafiya ba wani abu ne mai kyau ba

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku bayani kan cewa, yawan binciken lafiya ba wani abu ne mai kyau ba, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani kan cewa, kasar Sin tana ba da jagoranci ga fararren hula wajen aiwatar da manufar yin haihuwa bisa tsari ta hanyar daukar matakan ba da gatanci. To, yanzu ga bayanin.

A 'yan shekarun nan da suka gabata, a matsayin wata hanyar kiwon lafiya, ana fi dora muhimmanci kan yawan binciken lafiya. Amma kwararrun kasar Chile sun nuna cewa, yawan binciken lafiya zai ba da taimako wajen gano cuttuttuka a jikin mutum, amma a waje daya kuma zai kawo illa ga lafiyar jiki, shi ya sa yawan binciken lafiya ba wani abu ne mai kyau ba.

Jaridar kiwon lafiya ta kasar Chile da aka buga a ran 2 ga watan Janairu na shekarar da muke ciki ta ruwaito kwararrun aikin likitanci na kasar, cewa yanzu na'urorin yin binciken lafiya na zamani ne, kuma an kasa fannonin aikin likitanci kashi kashi masu yawa, sabo da haka an haifar da wasu matsaloli lokacin da ake binciken lafiyar jama'a, kamar yawan fannonin da ake bukatar yin bincike a kansu yana ta karuwa.

Game da likitoci dai, dogaro da sakamakon binciken lafiya wajen gano cuttuttukan da mutane suke fama da su ya fi yadda a kan dogaro da fasahohin jiyya. Sabo da haka, kila likitocin su kan bukaci a yi binciken lafiya ta fuskar likitancin kimiyya ga wasu mutanen da ke fama da kananan cuttuttuka kawai. Yanzu mutane sun fi mai da hankali kan yin binciken lafiya sakamakon kara fahimtar kiwon lafiya, kuma suna ganin cewa, idan aka yi binciken lafiya daga dukkan fannoni a lokaci-lokaci, to za a iya rigakafin kamuwa da cuttuttuka masu tsanani, sabo da haka, mutane masu yawa da ke da lafiya su ma sun fara yin binciken lafiya ba tare da gajiyawa ba.

Amma kwararrun Chile sun yi gargadin cewa, yawan binciken lafiya ba kawai zai kara yawan kudaden da fararren hula ke kashewa ba, har ma zai haddasa tashin hankalinsu, kamar nuna damuwa ko jin tsoro kan sakamakon binciken lafiya. Bugu da kari kuma binciken lafiya da ake yin amfani da haske iri daban daban mai karfi zai iya yin illa ga lafiyar jiki. Haka zalika kuma idan an yi binciken lafiya sau da yawa, to yiyuwar yin kuskure wajen tabbatar da cuttuttuka za ta karu. Sabo da haka watakila likitoci za su iya yin kuskure kan tabbatar da cuttuttuka sakamakon bayanai marasa kyau da aka samu sakamakon kuskuren na'urorin binciken lafiya.

Ban da wannan kuma kwararru sun ba da shawarar cewa, kafin a yi binciken lafiya, ya fi kyau a bukaci likitoci da su yi bayani kan matakan binciken lafiya, da kuma samun hanyoyin yin binciken lafiya maras hadari. Haka kuma sun jaddada cewa, ya kamata binciken lafiya ya zama wata hanya wajen kiwon lafiya a maimakon matsalar kawo barazana ga lafiya.

Jama'a masu sauraro, yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu yi muku wani bayani kan cewa, kasar Sin tana ba da jagoranci ga jama'a wajen aiwatar da manufar yin haihuwa bisa tsari ta hanyar daukar matakan ba da gatanci.