Daga yammacin karkarar birnin Shijiazhuang, babban birnin lardin Hebei na kasar Sin, ya kasance da wani tsohon gidan ibada na addinin Buddha, sunansa Pilusi, wanda ya shahara ne saboda ana adana zane-zanen jikin bango masu dogon tarihi da yawa a nan. A cikin shirinmu na yau, za mu ziyarci wannan gidan ibada, za mu more idanunmu da wadannan kyawawan zane-zanen jikin bango da aka kwatanta su da wadanda ke cikin kogon Mogao na Dunhuang.
An fara gina gidan ibada na Pilusi a zamanin daular Tang, wato yau da shekaru fiye da dubu 1 da dari 2 ke nan. Yawancin zane-zanen jikin bango da aka samu a nan a yanzu wadanda aka fito da su ne a farkon karni na 14, suna da daraja sosai a cikin dukan zane-zanen jikin bango na zamanin da da kasar Sin ta adana a yanzu. Fadin wadannan zane-zanen jikin bango na gidan ibada na Pilusi ya kai murabba'in mita 200 ko fiye, kuma an yi su ne da nagartacciyar fasaha bisa abubuwa da yawa, shi ya sa suna da daraja ainun a fannin fasaha, su ne daya daga cikin muhimman zane-zanen jikin bango da aka adana yadda ya kamata a kasar Sin a yanzu. A yayin da suka shiga cikin gidan ibada na Pilusi, da farko masu yawon shakatawa sun shiga cikin fada ta gaba, sunanta Shijia. An yi zane-zane masu fadin murabba'in mita 80 ko fiye game da labarun addinin Buddha da almarar gargajiya ta kasar Sin a jikin bangon fadar nan. Mai jagorar masu yawon shakatawa Mr. Tian Yatao ya bayyana cewa, addinan Buddha da Taoism sun saje dai dai da juna a cikin zane-zanen jikin bangon fadar Shijia.
Zane-zanen jikin bango sun fi nuna fasaha a cikin babbar fada ta baya mai suna Pilu, inda aka fi adana su cikin hali mai kyau. Ana iya kallon zane-zane mai fadin misalin murabba'in mita 120 a nan a yanzu, wadanda suka hada da mutane fiye da 500. Tian ya kara da cewa, dukan zane-zanen jikin bangon fadar Pilu na da labarunsu, kuma ko wane mutumin da ke cikin zane-zanen na da almara game da shi.
Siffofin mutane masu yawa da ke cikin zane-zanen jikin bangon fadar Pilu sun sha bamban da juna. Idan masu yawon shakatawa suna mai da hankulansu sosai, to, za su lura da cewa, zane-zanen jikin arewacin bangon fadar Pilu sun shafi batutuwan addinin Buddha, wadanda ke kan bangon fadar na gabas da yamma suna da nasaba da mutanen addinin Taoism, sa'an nan kuma, a kan bangon fadar na kudu, an yi zane-zane game da fararen hula.
An yi zane-zanen jikin bango a fadar Pilu ta hanyar gargajiya ta kasar Sin, fasahar masu zane na da kyau ainun, launuka na da kyan gani, mutanen da ke cikin zane-zanen suna kasancewa kamar yadda suke da rayuka. Hakazalika kuma, an yi amfani da fasahar musamman ta gargajiya ta kasar Sin wajen samar da zane-zanen jikin bango a fadar Pilu, ta haka zane-zanen na da kyan gani sosai da sosai.
Malam Tian ya yi karin haske cewa, (??3??)
'Saboda irin wannan fasahar musamman ta gargajiya ta kasar Sin, mutanen da ke cikin zane-zanen jikin bangon sun kara kasancewa da fasali mai kyau sosai, kuma sun kasance kamar mutane masu rai. An ce, da kammala aikin zane ke da wuya, sai wadannan zane-zane suka jawo hankulan mutane, kuma sun burge mutane sosai.'
Kyawawan zane-zanen jikin bango na gidan ibada na Pilusi sun jawo hankulan masu sha'awar zane-zanen jikin bango da kuma kwararru na gida da na waje, sun nuna babban yabo kan wadannan zane-zane masu daraja. Ko da yake a karo na farko ne da malam Zhang Zhen ya kai wannan gidan ibada ziyara, amma wannan nagartacciyar fasaha mai dogon tarihi ta burge shi sosai. Ya ce,(??4??)
'Ban yi tsammani cewa, a garinmu na Shijiazhuang mun sami irin wadannan zane-zanen jikin bango masu daraja hakan nan ba, har zuwa yanzu suna da kyan gani kwarai, sun kasance da na gaske ba, da cikakkiyar zuciya ce nake fatan za a adana su har abada, ta haka zuriyoyi masu baya da mu za su san dogon tarihi da magabatanmu suka samar.'
Ma'aikatan gidan ibada na Pilusi sun kiyaye wadannan zane-zanen jikin bango yadda ya kamata, amma abin bakin ciki shi ne saboda iska da yayyon ruwan sama, an cire wasu zane-zane daga bango. Darektan ofishin kula da gidan ibada na Pilusi malam Zhou Yanping ya bayyana cewa, (??5??)
'Bisa tushen yin nazari ta hanyar kimiyya, muna fatan za mu fito da dabara don kiyaye wadannan zane-zanen jikin bango ta hanyar kimiyya. Mummunan halin da zane-zanen jikin bangon ke ciki ba zai kara lalacewa ba bayan da muka dauki matakai. Ta haka za mu kiyaye su.'
To, jama'a masu sauraro, karshen shirinmu na yau ke nan, ni Tasallah da na gabatar nake cewa, ku huta lafiya.
|