Kamar yadda muka saba yi, da farko dai, za mu karanta muku wasu abubuwa kan wani shahararren titi da ke birnin Shanghai, sunansa Waitan, daga bisani kuma, sai wani bayanin musamman mai lakabi haka 'Ci abinci a titin Guijie na Beijing'.
A gabashin kasar Sin, wani kogi mai suna Huangpu ya ratsa birnin Shanghai, shi ne reshen kogin Yangtze. A yammacin bakin wannan kogi mai tsawon kilomita misalin 114, an shimfida titin Waitan tun daga titin Jinling a kudu zuwa gadar Waibaidu, ya kuma ketare koramar Suzhou a arewa. Yanzu ana yin amfani da kudin Sin misalin yuan biliyan 20 ko kuma dalar Amurka misalin biliyan 2.42 wajen tsabtace wannan korama, an kiyasta cewa, za a kammala wannan aiki a shekara ta 2010, aikin tsabtace wannan korama zai ba da taimako wajen maido da rayuwar kan ruwa a wannan yanki.
Tsawon titin Waitan ya kai misalin kilomita 1.5 gaba daya, da can an kira shi titin Huangpu. A lokacin da suke yawo a kan titin Zhongshan, masu yawon shakatawa na iya more idanunsu da kyawawan abubuwan masu dogon tarihi, saboda a can da manyan kamfanonin ciniki da bankuna sun gina hediwatocinsu a nan. A wani gefen wannan titi, kyawawan gine-gine da aka gina a shekaru 1930 na ci gaba da tsayawa, a wani daban kuma, kogin Huangpu na mallalawa a duk rana da dare.
A 'yan shekarun baya da suka wuce, an yi kwaskwarima kan titin Waitan. An kara tsayin bangon da ke datse ruwa don kiyaye birnin Shanghai daga ambaliyar ruwa. Mutane na iya jin dadin ganin kogin Huangpu a lokacin da suke yawo kan wannan bango mai fadi, sun kuma iya kallon gine-ginen zamani da aka gina a sabon yankin Pudong da ke kan gefe daban na kogin Huangpu.
Bayan ketare gadar Waibaidu, sai babban gida na Shanhai, wato Shanghai mansions a Turance. In ka tsaya a kan bene na 22 na wannan babban gini, to, ka iya fahimtar cewa, ashe, kana tsayawa a kan itatuwa, kuma a karkashin kafarka, ka iya ganin cewa, Shanghai cike yake da rububin mutane, wadanda suke kaiwo da dawowa.
Saboda manyan gine-ginen da aka gina bisa salon gine-gine iri daban daban a kan titin Waitan, shi ya sa an mayar da wannan titi tamkar bikin baje koli na gine-gine iri daban daban na duniya.
|