Bayan shagalin kaddamar da bikin "Shekara don kasar Sin", masu wasan kwaikwayo na kasar Sin sun nuna wa 'yan kallo na kasar Rasha wasu wasannin kwaikwayo da ke nuna halayen musamman na kasar Sin. Wasannin kwaikwayo na Beijing Opera da Chinese Kongfu suna nuna halayen musamman na kasar Sin sosai, kuma suna wakiltar al'adun kasar Sin. A gun shagalin ba ma kawai 'yan kallo na Rasha sun ji dadin wasannin kwaikwayo na Beijing Opera ba, har ma sun fahimci Chinese Kongfu. Sannan kuma, an nuna rawar Ballet mai suna "Tafkin Swan" ta kasar Rasha. 'Yan wasan ballet sun yi wannan wasa ne a kan kafadu da kawunansu. Bugu da kari kuma, 'yan wasan kwaikwayo na kasar Sin sun yi kida mai suna "Inuwar wata a cikin idon ruwa" da kayan goge na Erhu. Erhu, wani kayan goge ne na gargajiya na kasar Sin. Mu Sinawa muna sha'awarsa sosai.
Lokacin da ake wasan kidan "Inuwar wata a cikin idon ruwa", wannan kida ya ratsa zuciyar 'yan kallo na kasar Rasha. A waje daya kuma, lokacin da ake yin kida mai suna "Begen Rasha" da irin wannan kayan goge na kasar Sin, 'yan kallo na Rasha sun ji mamaki kuma sun yi tafi sosai.
Bayan da aka kawo karshen wannan shagalin nuna wasannin kwaikwayo na kasar Sin, 'yan kallo na kasar Rasha sun yi tafi har sau da yawa domin nuna wa masu wasan kwaikwayo na kasar Sin godiya. (Sanusi Chen) 1 2
|