Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-26 22:16:22    
'Yan majalisar CPPCC sun ba da shawara kan bunkasuwar tsarin jiyya na hadin gwiwa irin na sabon salo na kauyukan kasar Sin

cri

Rashin likitoci masu kyau da kuma rashin kudin ganin likita yana daya daga cikin matsalolin da ke damuwar fararen hula na kasar Sin a cikin 'yan shekarun da suka gabata. Kuma wannan matsala ta fi tsananta a kauyukan Sin inda tattalin arzikinsu yake baya baya. Domin kyautata matsayin jiyya na kauyuka, kasar Sin ta kaddamar da yin amfani da tsarin jiyya na hadin gwiwa irin na sabon salo na kauyuka bisa gwaji a shekara ta 2003 a wasu wurare, kuma an samu sakamako mai kyau. A gun taron shekara shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC da aka yi ba da jimawa ba, 'yan majalisar sun mai da hankali sosai kan batun da ke da nasaba da manoma. To, a cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku ra'ayoyinsu kan batun.

A kauyuka masu fama da talauci na kasar Sin, a kan ji tsoron kamuwa da cututtuka, dalilin da ya sa haka shi ne mutane masu yawa ba su da kudin ganin likita. Ko kuma ko da suna da kudin, amma ba su isarsu domin warkar da su kamar yadda ya kamata sakamakon matsayin jiyya maras kyau na wurin. Shi Xinmin, wani dan majalisar ya zo daga jihar Shanxi da ke arewa maso yammacin kasar Sin, kuma ya gaya wa wakilinmu cewa, "Garina yana cikin kauyukan kasar Sin, kuma yanzu iyayena suna zama a kauyuka. Na kan koma garina a ko wane wata, shi ya sa kullum na kan ga irin wannan hali, wato mutane ba su da kudi wajen shawo kan cuttuttuka masu tsanani, kuma ba safai su kan ga likita ba sakamakon kamuwa da kananan cututtuka, haka kuma ba safai su kan yi binciken lafiya ba. "

Kuma Mr. Shi yana ganin cewa, bayan da aka warware matsalar abinci da tufafi ta kasar Sin, matsalar ganin likita ta riga ta zama daya daga cikin matsaloli masu muhimmanci da manoman kasar Sin ke fuskanta. Amma an sassauta matsalar bayan da aka aiwatar da tsarin jiyya na hadin gwiwa irin na sabon salo na kauyuka.

Bisa matsayinsa na wani likita, furofesa Hou Shuxun, dan majalisar CPPCC yana kulawa da tsarin jiyya na hadin gwiwa irin na sabon salo na kauyuka. Kuma ya bayyana cewa, "Bayan da aka aiwatar da tsarin a kauyukan kasar Sin, an ba da tabbaci ga manoman da suka shiga tsarin wajen jiyya. Lokacin da suke kamuwa da cuttuttuka masu yaduwa, an iya warkar da su cikin lokaci kamar yadda ya kamata, haka kuma an iya rage nauyin da ke bisa wuyan iyalansu wajen kudade lokacin da suke kamuwa da cuttuttuka masu tsanani. Yanzu tattalin arziki na kauyukan kasar Sin ba ya samun ci gaba sosai, shi ya sa ina ganin cewa, a cikin wannan hali da ake ciki, aiwatar da tsarin wata hanya ce mai matukar kyau."

Bisa labarin da muka samu, an ce, ya zuwa watan Satumba na shekara ta 2006, an riga an kaddamar da aiwatar da tsarin jiyya na hadin gwiwa irin na sabon salo bisa gwaji a cikin rabin gundumomi da garuruwa na kasar Sin, kuma fararen hula da yawansu ya zarce miliyan 400 sun samu alheri daga tsarin. Lokacin da firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ke ba da rahoton aiki na gwamnatin kasar Sin a gun taron shekara shekara na majalisar dokoki ta kasar Sin, ya nuna cewa, za a ci gaba da aiwatar da tsarin a wurare mafi yawa a shekarar da muke ciki. Kuma ya kara da cewa, "Za a ci gaba da sa kaimi ga aiwatar da tsarin jiyya na hadin gwiwa irin na sabon salo na kauyukan kasar Sin. Kuma wuraren da za a aiwatar da tsarin bisa gwaji zai karu zuwa kashi 80 cikin dari na dukkan gundumomi da garuruwa na kasar Sin. A shekarar da muke ciki, gwamnatin kasar Sin za ta kebe kudaden taimakon da yawansu ya kai yuan biliyan 10.1, wato ke nan ya karu da yuan biliyan 5.8 idan an kwatanta shi da na shekarar da ta gabata."

Dan majalisar CPPCC Zhu Qingsheng ya taba rike da mukamin mataimakin ministan kiwon lafiya na kasar Sin, ya nuna amincewa sosai ga ci gaba da aiwatar da tsarin jiyya na hadin gwiwa irin na sabon salo na kauyuka da gwanmatin kasar Sin ke yi. Kuma ya bayyana cewa, 'yan majalisar CPPCC suna nuna kulawa sosai kan halin jiyya da kauyukan kasar Sin ke ciki, kuma sun gudanar da bincike har sau da yawa kan yadda ake aiwatar da tsari bisa gwaji, haka kuma sun bayar da shawarwari masu yawa kan batun. Yana ganin cewa, ra'ayin da firayim minista Wen Jiabao ya nuna kan tsarin jiyya na hadin gwiwa irin na sabon salo na kauyuka ba kawai ya bayyana kulawar da gwamnatin kasar Sin ke nuna kan batutuwan da ke da nasaba da fararen hula ba, har ma ya bayyana amincewar da gwamnatin kasar ke nuna wa shawarwarin da 'yan majalisar suka bayar a kan harkokin siyasa. Sabo da haka an ba su kwarin gwiwa sosai. Kande Gao)