Shugaba Hu Jintao na kasar Sin na yin ziyarar aiki a kasar Rasha tun daga yau zuwa ran 28 ga wata, bisa gayyatar da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin ya yi masa, inda zai halarci bikin kaddamar da 'shekarar al'adu ta kasar Sin' da kasar Rasha za ta shirya da dai sauransu. Kafin tashinsa, shugaba Hu ya zanta tare da kafofin yada labaru 6 na kasar Rasha da suka hada da kamfanin dillancin labaru na Interfax News Agency a nan Beijing. Shugaba Hu ya bayyana cewa, ya yi imani cewa, tabbas ne ziyarar da za ta yi zai samar da sabon karfin wajen zurfafa dangantakar da ke tsakanin Sin da Rasha. Ya ce,'Ina sa ran alheri kan shawarwarin da zan yi tare da shugaba Putin a lokacin da nake yin ziyara a kasar Rasha, inda za mu yi musayar ra'ayoyi kan zurfafa dangantakar hadin gwiwa da aminci da ke tsakaninmu bisa manyan tsare-tsare da habaka hadin gwiwarmu a dukkan fannoni da kuma sauran al'amuran da ke jawo hankulanmu dukka, sa'an nan kuma, zan halarci bikin bude 'shekarar al'adu ta kasar Sin' da na 'shagalin ciniki na kasar Sin'. Na yi imani cewa, tabbas ne zan sami sakamako mai kyau daga wajen ziyarata a wannan karo saboda kokarin da bangarorinmu 2 muke yi tare, haka kuma ziyarata za ta samar da sabon karfi wajen kyautata huldar kasashen 2 da sa kaimi kan hadin kanmu.'
Yanzu dangantakar da ke tsakanin Sin da Rasha ta kai matsayi mai ingantuwa da ba a taba ganin irinta ba a da. Sun sami sakamako da yawa daga wajen yin hadin gwiwa a fannoni daban daban. Sun kuma taimaka wa juna sosai a kan manyan al'amuran duniya da shiyyoyi, sun taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali na duniya.
Mr. Hu ya nuna cewa, a cikin sabuwar shekara, bangaren Sin na son gama kansa da bangaren Rasha wajen sa kaimi kan raya huldarsu daga fannoni 4. Ya ce,'Da farko ya kamata Sin da Rasha su karfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa, su ci gaba da fahimtar juna da goyon bayan juna a kan batutuwan da suka shafi babbar moriyar kasa. Na biyu, ya kamata su kara sa kaimi kan hada kansu a fannonin tattalin arziki da ciniki da makamashi da kimiyya da fasaha bisa ra'ayin moriyar juna da cin nasara tare. Na uku kamata ya yi su yi amfani da damar shirya bukukuwan 'shekarar al'adu ta kasar Sin' a Rasha, su habaka mu'amala da hadin gwiwa a fannin al'adun dan Adam, da kara fahimtar juna da aminci a tsakaninsu da jama'arsu. Na Hudu kuwa, kamata ya yi su kara taimakon juna kan batutuwan duniya da shiyyoyi bisa manyan tsare-tsare, su kara ba da gudummowa wajen kiyaye zaman lafiya na duniya da zabura samun bunkasuwa tare. Na yi imani cewa, tabbas ne ci gaban hudar hadin gwiwa da aminci da ke tsakanin Sin da Rasha bisa manyan tsare-tsare zai kawo wa jama'arsu da kuma jama'ar duk duniya fa'ida.'
A shekarun baya da suka wuce, Sin da Rasha dukkansu sun sami saurin bunkasuwar tattalin arziki mai dorewa, hakan ya samar da kyakkyawar dama gare su wajen hada kansu a fannin tattalin arziki da ciniki.
Game da kaddamar da harkokin 'shekarar al'adu ta kasar Sin' tare da shugaba Putin, Mr. Hu ya bayyana cewa,'Shirya 'shekarar al'adu ta kasa' a tsakanin juna,wato Sin da Rasha suke yi babban mataki ne da suka dauka don daukaka ci gaban huldarsu da sa kaimi kan sada zumunci a tsakanin zuriyoyin jama'arsu. Na yi imani cewa, irin wannan aiki zai kara wa kasashen 2 da jama'arsu fahimtar juna da aminci, zai kuma samar da sabon karfi a fannin raya huldar hadin gwiwa da abokantaka da ke tsakansu bisa manyan tsare-tsare.'
Shugaba Hu ya kara da cewa, Sin da Rasha sun mayar da juna a matsayin kasa mafi girma da ke makwabtaka da juna, jama'ar Sin na nuna matukar kona ga jama'ar Rasha.
Haka zalika kuma, shugaba Hu ya nuna kyakkyawan fata ga kafofin yada labaru na kasashen Sin da Rasha. Ya ce, bangaren Sin na sa kaimi da kuma goyon bayan kafofin yada labaru na kasashen 2 da su yi mu'amala da hadin gwiwa ta hanyoyi daban daban. Sin na maraba da manema labaru na Rasha da su watsa labaru kan kasar Sin yadda ya kamata bisa abubuwan gaskiya.(Tasallah)
|