Kabilar Tibet muhimmiyar kabila ce ga al'ummomin kasar Sin. Yawancin kabilar Tibet suna zama a tudun Qinghai-Tibet, wato suna zama a jihar Tibet mai cin gashin kanta da shiyyoyi da gundumomi na kabilar Tibet mai cin gashin kansu da ke lardin Qinghai da Gansu da Sichuan da Yunnan. Bisa kididdigar da aka yi a duk kasar Sin a shekara ta 2000, yawan mutanen kabilar Tibet ya kai fiye da miliyan 5 da dubu dari 4. 'Yan kabilar Tibet suna da yare da kalmomi da haruffan Tibet.
A da, an aiwatar da tsarin mulki na kama karya da ke hade da siyasa da addini a yankunan kabilar Tibet. Yankunan kabilar Tibet suna cikin al'ummar kama karya ta bauta. A karkashin mulkin tsarin kama karya na hade da siyasa da addini, yankunan kabilar Tibet suna koma baya wajen karfin kawo albarka. Suna noma Qingke,wani irin alkama. An kera kayayyakin yin aiki ne da karfe ko katako. Abin musamman da ya kamata in ambata shi ne, sana'ar kiwo da ake yi a tudun Qinghai muhimmiyar sana'a ce ta kabilar Tibet. Har zuwa yanzu, wannan sana'a ta fi aikin gona muhimmanci a yankunan Tibet. Dabbobin da 'yan kabilar Tibet suke kiwo suna da iri iri, ciki har da tumaki da awaki da shanu da dawaki da jaki da makamatansu.
Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, yankunan kabilar Tibet sun samu 'yancin kai bi da bi. Tun daga shekarar 1950 zuwa shekarar 1965, bi da bi ne aka kafa shiyyoyi da gundumomi na kabilar Tibet mai cin gashin kansu a lardunan Gansu da Qinghai da lardin Sichuan. A shekarar 1965, aka kafa jihar Tibet mai cin gashin kanta.
A waje daya kuma, masana'antu da zirga-zirga sun samu ci gaba a jihar Tibet. Bi da bi ne aka kafa masana'antun samar da wutar lantarki da na narke ingantaccen karfe da na kera injuna da hakar ma'adinai da na gine-gine da madaba'a da yin takardu da abinci a yankunan kabilar Tibet. Sana'ar hannu ma ta samu cigaba sosai. Kafin kafuwar jihar Tibet mai cin gashin kanta, zirga-zirgar jihar tana koma baya sosai, babu hanyar jiragen sama da ta jirgin kasa. Amma, yanzu, bi da bi ne aka shimfida hanyoyin mota da ke hade da jihar Tibet da lardin Qinghai da Sichuan da Xingjiang da lardin Yunnan da wasu hanyoyin mota da ke hade da jihar da kasashen waje. Kusan kowace gunduma tana da hanyoyin mota. Sa'an nan kuma, an bude hanyoyin jirgin sama da ke hade da jihar da birnin Chengdu da Beijing da Lanzhou da birnin Kathmandu na kasar Nepal. A ran 1 ga watan Yuli na shekarar 2006, an kaddamar da hanyar dogo da ke hade da birnin Lhasa da birnin Germu na lardin Qinghai. Sakamakon haka an canja halin rashin hanyar dogo da ake ciki a jihar Tibet.
Yanzu, matasan kabilar Tibet suna neman ilmomi iri iri a jami'o'in da ke sauran yankunan kasashen Sin. An kuma kafa jami'o'i iri iri a jihar Tibet, ciki har da jami'ar Tibet.
Yawancin 'yan kabilar Tibet suna bin addinin Bhuda.
|