Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-26 15:46:06    
Ana kokarin neman shimfida zaman lafiya a gabas ta tsakiya

cri

A cikin shirin nan za mu kawo muku wani labarin da wakilin gidan rediyo na kasar Sin ya rubuto mana kan yunkurin da ake yi domin shimfida zaman lafiya a GTT.

A ran 25 ga wata babban sakatare na MDD Mr Ban Ki-moon da sakatariyar harkokin waje ta Amurka Cobndoleezza Rice dake ziyara a gabas ta tsakiya sun kai ziyara a Palastinu bi da bi,kuma za su gana da shugabannin Isra'ila.A ganin kafofin yada labarai, burin ziyarar da wadannan manyan mutane biyu suka yi a Palastinu da Isra'ial,shi ne ciyar da shawarwarin shimfida zaman lafiya tskanin Palastinu da Isra'ila gaba.Duk da haka matsayin da shugabanni na Palastinu da Isra'ila suka dauka kan batun sakin mutanen da aka tsare sun saba wa juna,don haka da wuya a ce kokarin da Ban Ki-moon da Condoleezza Rice ke yi zai sami nasara ko a'a.

Palastinu kasa ce ta farko da Mr Ban Ki-moon ya fara yada zango a cikin ziyararsa a gabas ta tsakiya.A ran 25 ga wata ya tattauna da shugaban hukumar mulkin kan al'ummar Falastinawa Mahmoud Abbas a garin Ramallah.Bayan haka Condoleezza Rice wadda ta gama ziyararta a kasar Massar ta na bayansa,ita ma ta yi shawarwari da Abbas.Sannan Ban Ki-moon da Condoleezza Rice sun gana cikin gajeren lokaci a birnin Mukkadas.Bisa shirin da aka tsara,kowanensu zai gana da firayim minista na Isra'ila Mr Ehud Olmert a ran 26 ga wata.

Manyan shugabannin nan biyu suna fatan a kafa wata gwamnatin hadin gwiwa a kasar Palastinu a cikin ziyararsu.A shirye suke kasashen Larabawa su kira taron shugabanni domin gano bakin zaren ciyar da shawarwari tsakanin Palastinu da Isra'ila gaba ta yadda za a shimfida zaman lafiya a gabas ta tsakiya.Bayan da ya gana da Abbas,sakatare-janar Ban Ki-moon na MDD ya ce yanzu wani muhimmin lokaci ne,da ya ke da akwai siratsi a gaba,kamata ya yi a yi amfani da wannan lokaci a ciyar da gwagwarmayar shimfida zaman lafiya gaba.Condoleezza Rice ta bukaci Isra'ila da Palastinu da su tsara wani shirin aiki na tarayya ta yadda za a iya tabbatar da kafuwar kasar Palastinu.Ta ce wani burin tarayya na taimakawa bangarorin da abin ya shafa.Bisa labarin da aka samu,an ce Rice ta yada zango a Palastinu da Isra'ila cikin wannan ziyara,ta gana da Abbas da Olmert.Ta ce ta yi fatan shugabanni na bangarori biyu su yi musayar ra'ayoyi da samu matsayin daya da fahimtar sassaucin da kowanensu zai yi,daga bisani za su yi tattaunawa kan zaman lafiya.

Yayin da Ban Ki-moon da Condoleezza Rice ke kokarin sa kaimi kan gwagwarmayar shimfida zaman lafiya a gabas ta tsakiya,su ma sun amince da cewa da wuya a samu babban cigaba kan batun nan a halin yanzu.Dalili kuwa shi ne sabuwar gwamnatin Palastinu ba ta biya bukatun bangarori hudu ciki har da MDD kan batun gabas ta tsakiya na cewa a amince da Isra'ila da a yi watsi da karfin tuwo da yin aiki da yarjejeniyoyin da Palastinu da Isra'ila suka daddale.Firayim ministan Isra'ial ya fito fili ya yi adawa da sabuwar gwamnatin,ya ki yin shawarwarin shimfida zaman lafiya tsakaninsa da Abbas.Bisa halin da ake ciki,Mr Ban Ki-moon ya ce lokaci bai yi ba da za a yi shawarwari da jami'an Hamas a yanzu.

Yayin da Mr Ban Ki-moon da Condoleezza Rice ke ziyara domin ciyar da shawarwarin tsakanin Palastinu da Isra'ila gaba,bangarori biyu Falastinu da Bani Isra'ila sun fara wani sabon zagaye na cacar baka.A gun taron da aka saba yi na majalisar ministoci na kasar Isra'ila a ran 25 ga wata,firayim ministan Olmert ya yi suka ga Abbas cewa ya karya alkawarin da ya dauka a fili kan Isra'ila,musamman kan alkawarin sakin wani sojin Isra'ila da ake kira Gilad Shalit da kungiyar dakarun Palastinu ta sace kafin kafa sabuwar gwamnatin Palastinu.Olmert ya kuma ce wannan aikin da Abbas ya yi ba zai taimaka ba wajen musayar ra'ayoyi tsakanin Isra'ila da hukumar mulkin kai ta al'ummar Falastinu.Wani jami'in Palastinu ya ce Abbas bai taba daukar alkawari kan batun nan ba ko makamantansa.ya ce zai yi iyakacin kokarinsa wajen neman saki Gilad Shalit.A wannan rana Abbas shi kansa ya bayyana cewa dole ne Isra'ila ta yi la'akari da batun saki Falastinwa da ta tsare.Ministan watsa labarai na Palastinu Mustapha Balguti shi ma ya la'anci Olmert da cewa ya rudi hankulan kasashen duniya da na mutanen Isra'ila.Ya kuma ce ya kamata Isra'ila ta dauki alhakinta kan ba a saki Gilad Shalit cikin lokaci ba,dalili kuwa shi ne Isra'ila ba ta nuna natsuwa kan shawarar da Palastinu ta gabatar game da musayar mutanen da aka tsare.Lalle cacar baka da shugabanni na Palastinu da Isra'ila suka yi kan batun nan ba zai kulla kome ba illa zai janyo mugun tasiri ga kokarin da Mr Ban Ki-moon da Condoleezza Rice suke yi domin ciyar da gwagwarmar shimfida zaman lafiya a gabas ta tsakiya gaba.

Jama'a masu sauraro,wannan ya kawo karshen shirinmu na yau,sai ku cigaba da sauraron shirye-shiryenmu.///