Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-23 16:47:21    
An samu sakamako a gun taro na matakin farko na shawarwari na zagaye na shida tsakanin bangarori shida

cri

An yi shelar dakatar da shawarwari na zagaye na 6 tsakanin bangarori 6 kan batun nukiliyar zirin Korea bayan da aka zartar da ' Sanarwar shugaba' a ranar jiya Alhamis. Mr. Wu Dawei, shugaban shawarwarin kuma jagoran tawagar wakilat ta bangren kasar Sin ya yi hasashen, cewa an samu sakamako mai kyau a gun taro na matakin farko na shawarwarin tsakanin bangarori shida. Yayin da yake shelar dakatar da shawarwarin ya fada wa manema labaru cewa : 'Bangarori daban-daban sun yarda da ci gaba da ingiza yunkurin shawarwarin tsakanin bangarori shida; Ban da wannan kuma sun sake nanata cewa za su sauke nauyi cikin tsanank dake bisa wuyansu na aiwatar da ' Sanarwar hadin gwiwa ta 9.19' da kuma takardar hadin gwiwa kan ' Matakin farko na aiwatar da sanarwar hadin gwiwa'; Kana bangarori daban-daban sun yarda da dakatar da shawarwarin cikin gajeren lokaci da kuma maido da shi tun da wur-wuri domin ci gaba da yin tattaunawa kan yadda za a dauki matakin nan gaba na aikawarta.

An soma yin wannan shawarwari ne a ran 19 ga watan da muke ciki a nan birnin Beijing. A cikin kwanaki 4 da suka shige, bangarori daban-daban sun saurari rahotanni da kungiyoyin aiki guda biyar suka gabatar. Bayan haka, sun yi tattaunawa sosai kan daukar matakin farko da kuma tsara shirin aiwatarwa na matakin nan gaba. ' Ba za a iya ci gaba da gudanar da shawarin ba' cewar da Korea ta Arewa ta yi,' sai dai idan an sake kudadenta da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan ashirin da biyar da take da su a Bankin Delta Asia na Macao cikin ajiyar banki na kasar Sin. Lallai ana bukatar samun wasu lokuta don warware wannan magana. Saboda haka ne, aka yi shelar dakatar da shawarwari na wannan zagaye bayan an jinkirtar da shi cikin yini daya, wanda kuma aka shirya gudanar da shi cikin kwanaki uku. Amma Mr. Wu Dawei ya furta ,cewa babu tantama an samu sakamako mai kyau a gun shawarwari na matakin farko. Ya kuma jaddada, cewa da yake bangarori shida suna bukatar samun moriya iri daya, don haka za su gamu da wassu matsaloli iri daban-daban a cikin yunkurin shawarwarin. Mr. Wu Dawei ya kara da, cewa akan samu bambancin ra'yoyi masu tsanani kan maganganu da dama a gun shawarwari na kowane zagaye da aka yi a da. Amma mun samu babban ci gaba sakamakon kokarin da muka yi cikin wani lokaci.

Mr. Gao Hong, kwararren Kolejin nazarin kimiyya da zamantarewar al'umma na kasar Sin a fannin al'amuran kasa da kasa ya bayyana ra'ayinsa, cewa: ' A ganina, dakatar da shawarwari cikin gajeren lokaci ba zai kawo cikas ga babban yunkurin shawarwarin tsakanin bangarori shida ba domin da zarar an shiga mataki na zahiri tilas ne za a gamu da matsaloli da yawa. Idan an bi wata hanya daban a waje da taron shawarwarin wadda kuma ta fi saukin warware batun nukiliyar zirin Korea, to labuddah wannan taka muhimmiyar rawa wajen daukaka ci gaban yunkurin shawarwarin wanda za a maido da shi'.

Mr. Wu Dawei ya sa ran alheri ga shawarwarin tsakanin bangarori shida. Ya fadi, cewa: ' A gun taron shugababannin tawagoyin da aka kawo karshensa dazu-dazun nan, mun sake lashi takobin daidaita wannan batu. Mun yi imanin cewa za mu iya gano bakin zaren da zai dace da warware wannann magana. Mun hakkake, cewa za a gudanar da shawarwarin tsakanin bangarori shida lami-lafiya, kada a yi shakka kan makomar shawarwarin domin muna da karfin haye wannan wahala. Labuddah shawarwarin na da kyakkyawar makoma'. ( Sani Wang )