Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-22 15:11:21    
Kan yadda aka samu shawarar da 'yan majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa na kasar Sin (Babi na biyu)

cri

Majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin wata hukuma ce mai muhimmancin da ke karkashin jagorancin Jam'iyyar Kwaminis ta Sin kan hadin kan jam'iyyun siyasa da dama da ba da shawarwari kan harkokin siyasa,muhimman ayyukanta ne ba da shawarwari kan harkokin siyasa da sa ido ta hanyar demakuradiya da kuma shiga harkokin siyasa,muhimman hanyoyin da jam'iyyun siyasa da kungiyoyi da manyan mutane na da'irori da na kabilun dabam daban ke bi wajen shiga harkokin siyasa da taka rawa bisa tsarin siyasa na kasar Sin.Yin bincike da nazari da kuma tattaunawa da ba da shawarari kan muhimman batutuwa a fannonin siyasa da tattalin arziki da al'adu da zamantakewa da mutanen Sin suke sa lura a kai ga hukumomi na jam'iyyar kwamins ta Sin da na gwamnati,muhimman ayyuka ne namajalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa na kasar Sin.

Mr Zhou Shaolai,masani na ofishin nazarin harkokin siaysa na cibiyar nazarin kimiyyar ilmin siyasa ta kasar Sin ya ba da ra'ayinsa kan shawarar da aka dauka cikin takarda ta farko ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin ya ce "shiga harkokin siyasa da tattauna batutuwa da 'yan majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa suka yi,muhimman ayyuka ne wajen raya kasa.duk wanda suke yi na ba da shawarwari da bincike da kuma rangadi duk domin neman samun cigaban zamantakewar kasar Sin.Wannan ya kuma ba da shaida cewa matsayin 'yan majalisar ba da shawarwri ya kara dagowa kuma sun kara taka rawa a kasar Sin.Muddin suka ba da shawarwari masu amfani da hanyoyin da za a bi dangane da bunkasuwar kasa da zaman jama'a,kwamitin tsakiya na iya daukar shawarwarin da suka bayar cikin manufoffi da ka'idojin da aka tsara.

Kun dai saurari wani labari ne da wakiliyarmu ta rubuto mana kan yadda kwamitin tsakiya na kasar Sin ya dauki shawarar da wani dan majalisar ba da shawarwari ta kasar Sin ya bayar a cikin takarda ta farko ta kwamitin tsakiya,duk da haka shi yana daya daga cikin daruruwanshawarwari da 'yan majalisun suka bayar wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa kasar Sin.Bisa labarin da muka samu,tun daga zama na hudu na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta jama'ar Sin a karo na goma har zuwa zama na wannan shekara,kashi 98da digo 94 cikin dari na shawarwarin da aka bayar an ba su amsa.

A ganin masani Mr Zhou Shaolai,amsar da aka bayar kan shawarwarin da 'yan majalisar ba da shawarwarin suka bayar,ya shaida cewa shawarwarin da suka gabatar na da inganci kuma sun shafi muhimman batutuwa na jama'ar kasar Sin.A sa'I daya kuma ya shaida cewa 'yan majalisar sun kara taka muhimmiyar rawa wajen tsara manufoffi na jam'iyya da na gwamnati.

A ganin Mr Han Xu,masani na ofishin nazarin harkokin siyasa na cibiyar nazarin ilmin kimiyyar zamantakewa ta kasar Sin,wannan muhimmin tsarin siyasa na ba da shawarwari kan harkokin siyasa na majalisar ba da shawarwari da na jam'iyyun siyasa da dama bisa hadin kai yana nan yana taka muhimmiyar rawa.Ya ce "majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa wata muhimmiyar hukuma ce da take taka muhimmiyar rawa wajen shimfida siyasar demakuradiya a kasar Sin.kamata ya yi a dauke ta wani cigaban kasar Sin wajen bunkasa siyasar demakuradiya a kasar Sin kuma nasara ce da muka samu."(Ali)