Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-21 17:44:05    
Sharhin masu sauraronmu a kan manyan tarurruka biyu na kasar Sin

cri

Jama'a masu sauraro, barkanku da war haka, barkanmu kuma da saduwa da ku a zaurenmu na "amsoshin wasikunku", inda muke karanta wasikun da ku masu sauraronmu kuke aiko mana, tare kuma da amsa tambayoyin da kuka sa a ciki, kuma ni ce Lubabatu ke gabatar muku da wannan shiri a duk ranakun Lahadi daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin.

Masu sauraro, tun daga ran 3 har zuwa ranar 16 ga watan nan da muke ciki ne, aka shafe kwanaki 13 ana yin babban taron shekara shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin da na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a nan birnin Beijing, inda aka tattauna muhimman batutuwan da ke shafar tattalin arziki da zaman al'umma da dai sauran fannoni daban daban na kasar Sin. Tarurrukan dai sun kasance al'amari mai matukar muhimmanci a harkokin siyasa na kasar Sin. Kwanan nan, bayan da masu sauraronmu suka sami labarin wadannan tarurruka guda biyu, sai bi da bi ne suka aiko mana ra'ayoyinsu a kansu.

Malam Mamane Ada daga birnin Yamai na jamhuriyar Nijer ya rubuto mana cewa, kasa kamar kasar Sin ta dace a ce tana irin wadannan tarurruka, domin magabatan wannan kasa su san inda daki ke musu yoyo, domin daukar matakai na gyara jin dadin rayuwar Sinawa. Bayan haka, kasar Sin ta shaida wa al'ummarta yadda take tafiyar da siyasarta da sauran kasashe na duniya da suka hada da neman dangantakar kasuwanci, neman zaman lafiya a doron duniya, taimaka ma kasashe masu tasowa da kuma samun goyon bayan kasashe a majalisar dinkin duniya, idan abu ya shafi ci gaban kasashe da na al'umma, amma duk wadannan sai da shawara ta 'yan kasar Sin maza da mata. Don haka, tarurrukan suna da riba har ga duniya baki daya.

Sai kuma malam Bala Mohammed daga birnin Abuja, tarayyar Nijeriya, ya ruwaito mana cewa, ina taya jama'ar Sin murnar bude wannan babban taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, wato hukumar koli ta dokokin kasar Sin, a Beijing babban birnin Kasar Sin, da kuma fatan za a tattauna muhimman abubuwan da suka shafi jama'ar kasar da kuma sauran duniya. Ina kuma fatan za a gama lafiya a kuma watse lafiya. Ina ganin zai yi kyau idan kasashe masu tasowa musamman na Afirka za su yi koyi da wannan tsari wajen tafiyar mulkin dimokradiyarsu. Domin wannan tsari ne wanda yake ba talakawa damar sanin yadda ake tafiyar da harkar mulki, kuma wata kafa ce da ta ba jama'a damar tofa albarkacin bakinsu a kan harkokin mulki. A kullum kasar Sin tana kasancewa jagaba ne ga kasashen duniya wajen tafiyar da sahihin tsarin mulki, ciniki da kuma zamantakewa, saboda haka Allah ya sa shugabannin Afrika za su yi koyi da irin wannan kyakkyawan tafarki, amin.

Bayan haka, a cikin Email da malam Mahaman Salisu Elh Hamisu daga jamhuriyar Nijer ya rubuto mana, ya ce, duk wata kasar da ta san 'yanci da martabar al'ummarta, ya kamata a ce tana gudanar da irin wadannan tarurruka na majalisu da ke dauke da nauyin wakilcin al'ummarta, domin ta haka ne kawai mahukunta za su san me ya kamata su yi wa jama'ar da suke mulka wajen kara inganta rayuwarsu, da kuma auna karfin tattalin arzikin kasar tare da sake shimfida wasu sababbin dabaru ta fuskar siyasar ciki da wajen kasa, sabo da haka, irin wannan taro na majalisun kasar Sin yana da matukar amfani.(Lubabatu)