Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-21 17:24:53    
Daga Bala Mohammed

cri
Gaisuwa mai yawa tare da fatan alheri ga daukacin jama\'ar kasar Sin. Ina kuma fatan duk ma\'aikatan gidan rediyon Kasar Sin suna cikin koshin lafiya.

Bayan haka ina taya jama\'ar Sin murnar bude wannan babban taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama\'ar kasar Sin, wato hukumar koli ta dokokin kasar Sin, a babban birnin Kasar Beijing, da kuma fatan za\'a tattauna muhimman abubawan da suka shafi jama\'ar kasar da kuma sauran duniya. Ina kuma fatan za\'a gama lafiya a kuma watse lafiya.

Ina ganin zai yi kyau idan kasashe masu tasowa musamman na Afirka zasu yi koyi da wannan tsari wajen tafiyar mulkin dimokradiyar su.

Domin wannan tsari ne wanda yake ba talakawa daman sanin yadda ake tafiyar da harkar mulki,kuma wata kafa ce ta ba jama\'a daman tofa albarkacin bakinsu a kan harkokin mulki.

A kullum kasar Sin tana kasancewa jagaba ne ga kasashen duniya wajen tafiyar da sahihin tsarin mulki, ciniki da kuma zamantakewa, saboda haka Allah ya sa shugabannin Afrika za su yi koyi da irin wannan kyakkyawan tafarki, amin.